Yadda Zakayi Transfer Na Data MB A Layin MTN Cikin Sauki
Ga wata Sabuwar Damar Da Zaku Samu ₦50,000 Daga FirstBank tare da (Sanlam)
Jama’a Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
A yau zanyi muku bayani akan yadda zakuyi transfer na data mb a layin mtn cikin sauki, wato yadda zaku turawa abokin ku data daga layin ku zuwa layinsa.
Wani lokacin kukan samu data a layin ku imma abaku kokuma ku saya wanda idan kai kadai zakayi amfani da ita baza ka iya karar da itaba har lokacin expire ta yayi, amma idan ka samu dama zaka iya turawa abokinka domin duk kuyi amfani da ita.
Idan kanason turawa wani data daga layin ka na mtn zuwa na abokinka ga yadda zakayi:
Da farko ka tabbatar akwai datar a wayan naka domin zaka iya tura masa daga 100mb har zuwa 2GB.
Bayan ka tabbatar akwai mb din a layin ka, yanzu saika danna *131*7# daka danna zai kawo maka zabi sai Jay Replay da 1
Daga nan zai kawo ka inda zakasa number wanda zaka turawa data mb din sai ka sanya number sa
Daga nan zai nuna maka jerin datan da zaka iya tura masa, saika zaba ka tura masa
Daga nan shikkenan ka tura masa data mb nan take zaiji sakon message ka tura masa data mb.
Shikkenan sannan kuma datan zatayi expire ne dede lokacin da takan zatayi expire.
Sannan kuma kamar yadda ake duba kowace data itama haka ake duba ta wato * 131 * 4 #
Allah ya bada sa’a