Yadda zaku canja bayanan BVN idan kunyi kuskure a baya

Asalamualaikum Barkan mu da sake saduwa a wanan lokacin Mai albarka ,a insha Allahu darasin mu na yau shine yadda zaku Sanja bayanan BVN kamar shekarar haihuwa da lambar waya.
Mutane da dama suna fama da matsala a Kan bayanan su na BVN wasu lokacin da suka cike Basu ban ainahin shekaran da aka haife su ba wasu Kuma Wanda suka je wajensa cikewa shine ya musu ba Dede ba da dai makaranta irin wadannan matsaloli.
To kada KU damu idan har Kun samu kanku a daya daga cikin wadannan matsaloli ga hanyar da yakamata kubi Wajen Magance ta.
Wannan hanya ba Wata hanya bace Mai wahala zaku iya Yi da wayar dakuke amfani da ita ta Android cikin sauki ku samu kome naku ya dedeta ba Sai kunje banki ba.
Ita de Wannan hanyar, hanyace da ake aika sako zuwa ga Gmail address me sunan Nibss.
Kafin mu cigaba ya kamata ku San mine Nibss yake nufi
Domin share tantama saboda wasu zasu iya zargin wannan damfara ne saboda anyi maganar BVN Wanda ba haka bane a taikace Nibss a turance Yana nufin Nigeria Inter-Bank Settlement System Plc NIBSS Wata ma’aikata ce Wanda suke kula da harkokin banki tare da kula da hakkin kwastomomin su. Shine suka ga ya dace su fidda wannan tsarin domin ragewa bankuna aiki tare da saukakawa kwastomomi basai kana Zuwa bankin ka ba zaka iya Yi kana gida.

Yadda zaku tura wannan Gmail address na gyaren BVN zai kasance kamar haka:-
Zaka Shiga manhajar Gmail address kaje Wajen rubuta sako awajen me karban sakon zaka rubuta  info@nibss-plc.com.ng,
Sai Kuma naka me turawa Wanda yawanci kana Shiga zakaga sun Nuno maka shi.
A Wajen subject na Gmail Kuma saiku rubuta: change of date of birth idan shi zaku Sanja idan Kuma number waya ce saiku rubuta change of phone number.
Sai Kuma kuyi sakin layi ku rubuta:-
I lost my bvn phone number as a result of my phone being stolen, I need change my phone number. Wannan ga Wanda zasu nemi a Sanja musu number waya ce misali a cikin zaku rubuta dalilin dayasa zaku Sanja number wayar shin Bata tayi, ko wayarka aka sace, ko Kuma gidan layi ne suka rufe maka shi.

Ga Wanda zasu nemi na BVN zaku rubuta kamar haka a misalance, I want change my date of birth because I make a correction in my previous date of birth.
Anan zaku Yi bayanin dayasa kuke son Sanja date of birth naku.

Sannan zaku Basu bayanan BVN naku kamar haka wannan misali ne gamasu sanja shekarar haihuwa.

misali
BVN: 12345***
First name: zainab
Last name: isa
Middle name: musa, idan da suna biyu kake amfani ba ruwanka da saka middle name.
Phone number:.09131722855
Old date of birth: 01/01/2022
New date of birth 24/08/1999
Sannan zaku hada da photo na declaration of age Wanda aka Sanja muku shi ko affidavit na kotu Wanda aka Sanja muku shekaran ta haihuwa.

Ga masu Sanja number waya Kuma zasu tura ne kamar haka:-
BVN:223455*
First name: ginsau
Last name: sani
Date of birth: 22/08/2/2002
Old phone number: 08080799297
New phone number: 09131722755

Sannan zaku hada da photo na kadin haihuwa ko katin zabe Wanda ya nuno Kun mallaki wannan sabuwar number Kuma wannan bvn taku ce.
Daga Nan saiku aika sakon zaku jira kuga har Zuwa lokacin da zasu tuntube ku.

Allah ya bada nasara ameeen.

kudai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

mungode ???

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!