Ga Wasu Hanyoyi 5 Da Zaku Samu Kudi Da Wayar Ku A Wannan Shekarar 2023

Assalamu alaikum warahamatullah,  barkanmu da sake kasancewa damu a wannan shafin namu mai albarka.

A yau nazo muku da wasu ingantattun hanyoyi guda biyar da zaku iya fara samun kudi dasu ta hanyar amfani da wayar ku ta android ko iphone.

Kamar de yadda wasun ku suka sani samun kudi da wayar android ko iphone ba wani sabon abu bane domin abu ne da aka jima anayi akwai dubbannin mutane da sukayi kudi kuma suke samun kudi ta hanyar amfani da wayar su, sai de nasan duk da hakan har yanzu akwai wadanda basusan ana samun kudi da waya ba kokuma basu yarda ba,  wanda wanann tsohon abune a wajen wasu.

Amma duk da haka yau zan kawo muku hanyoyi 5 da ake samun kudi da wayar android ko iphone,  kuma kudi mai yawa wanda a kalla zakana iya samun kimanin 50,000 aduk wata ko fiye da hakama, domin akwai masu samun sama da million aduk wata kuma ta hanyar amfani da wayar android.

Dan haka ga hanyiyin guda biyar zan jerosu sannan zanyi bayanin kowannen su.

  • Blogging
  • Youtube
  • Affiliate Marketing
  • Freelancer
  • Social Media/ Handle Manager

Wadannan sune hanyoyi guda biyar dana zakulo muku wanda zaku iya samun kudi dasu da wayar ku, sannan kuma wadannan ba sune kadai hanyoyiba akwai hanyoyi dayawa da ake samun kudi da wayar android,  amma de wadannan suna daga cikin wadanda akafi amfani dasu,  dan haka yanzu zanyi bayanin kowanne a takaice saiku duba kuga wanda ya kamata ku fara domin fara samun kudi da wayar ku.

  • Blogging: Ita wannan Blogging ɗin wata abace wacce ake aiwatar da ita a yanar gizo, a inda mutum ze dauki wani bangare na ilimi, musamman abunda yafi kwarewa akai, Yanayin rubutu akan waɗannan ababe domun yasama mabiya waɗan da zasu dinga karanta wannan rubutu nasa. Abin da blog ya kunsa, yawanci yakanzo ne ta hanyar labarai akan ita shafin yanar gizon wanda mutum ke rubutawa da ake kira blogs posts. Abubuwan da kake karantawa a yanzu haka, shine misalin wannan Blog posts din.

Ta wannan hanyar ana iya samun makudan kukade,  domin zaka iya tsara website dinka sannan ka nemi tallah daga kamfanin google wanda zasu duba su gani idan site din naka ya cika ka’idar da sukeso saisu amince dakai,  daga nan zaka fara samun kudi masu yawa a duk wata inde kayi aiki.

A kwai darasi na musamman danayi akan yadda zaka kirkiri blog/website da kanka har takai inda zaka fara samun kudi.  Idan nason koya danna Link dake kasa

Yadda zaka kirkire website/blog da kanka

  • Youtube: shima daya ne daga cikin manyan kamfani da suke yada sakonni ta hanyar video,  yana daya daga cikin kamfanin da yafi kowane tarin mabiya masu dora video a akansa, sannan yana bada dama kowane mutun ya mallaki channel a karkashinsa domin ya samu damar dora dukkan videon daya gadama,

Sannan kuma ya bada wasu kaidoji ga duk wanda yakeson fara samun kudi a karkashinsa,  hakanne yasa shima yake kan gaba wajen hanyar samun kudi dashi ta hanyar amfani da wayar ka.

Dan haka shima akwai darasi na musamman dana ware kuma na koyar tun daga yadda zaka bude shi ka mallaki channel ka fara samun kudi da ita.

Dan haka idan kana bukata saika danna link dake kasa

Yadda zaka fara samun kudi da youtube

Sabo da kar rubutun yayi tsayi zamu raba rubutub gida biyu domin a samu sauki wajen karantashi kuma a fahinta.

Dan haka ga karashen rubutun saiku danna Nan domin ku karanta sauran rubutun

Darasi na biyu – Yadda ake samun kudi da waya

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!