yadda zaku Kara girman memorin wayarku zuwa 1024Gb

Assalamu Alaikum yan uwa barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan lokacin a yau nazo muku da wani sabon Application mai matukar amfani wanda na tabbata inshallah zai burge ku.

WANNAN WANI APPLICATION NE 
sunan wannan sabon Application Terabox yana da matukar amfani zai temaka ma wajan karawa memorin wayarka girma idan memorin kan wayarka bashi da girma ko kuma kana saurin cika shi to wannan App din zai temaka ma domin shima memori ne mai zaman kansa yana da 1024GB space idan kana amfani da wayarka memorin kanta ya cika kuma kana son tura wasu abubuwa masu muhimmanci to zaka iya amfani da wannan muhimmin Application din.

ABIN BIRGEWA GA WANNAN APP DIN 
Idan ka tura abubuwan ka masu muhimmanci a cikin wannan sabon App din koda wayarka ta bata ko an sace kana siyan sabuwar waya daka sauke Application din kana sa email dinka da password dinka zai bude za kaga komai naka daka ajiye acikin sa idan kuma kana da yawan manta password zaka iya joined dinsa da Fecebook Account dinka hakan zai kara saukaka maka.

YANDA AKE BUDE WANNAN APP DIN 
daka ka shiga Application din zai kawo ma zabi guda biyu kana son abude App din da email address ko kana son joined din sa da Fecebook Account dinka
idan kana son bude shi da email address kana danna yanda aka sa Log in with Google zai kawo ma yanda zaka sa email din ka tare da yanda zaka sa password kana sawa zai kawo ma continue dana danna continue App zai nemi ka bashi damar amfani a wayarka ta hanyar danna Allow wannan App din ya kawo ma kana gama zaka ga App din ya bude idan kuma Fecebook Account dinka kake son bude wa zaka danna logon Fecebook kana danna wa zai kawo ma sunan ka wannda ka bude Fecebook idan da Fecebook a wayarka misali zai tambayeka continue as Yuseep_Tv sai ka danna continue kana danna wa App din zai nemi ka bashi damar aiki a wayar ta hanyar danna Allow daya kawo ma kana gama danna wa App din zai bude.

YANDA AKE AJIYE HOTO KO VIDEO A CIKIN WANNAN APP DIN
kana shiga cikin Application din daka kasa zakaga wata alamar plus ta bayyana kana danna ta zai kawo ma zabi biyu upload da remote upload saika danna upload kana danna wa zai kawo ma dukkanin hotuna da video wanda suke cikin wayaka saika zabi hoto ko video wanda kake son ajiyeshi ka danna kansa daka danna kansa hoton ko videon zai fara upload amma zai kawo ma zabi biyu use cellular data kana son yin amfani da datar wayarka wajan ajiye wannan hoto ko wait for wifi ko kuma zaka jira sai an kuna wifi yayi uploading saika zabi wanda kake so kana zaba take zaiyi uploading ya shiga cikin App din.

IDAN KANA SON DOWNLOAD DINSA

Danna nan

Kai tsaye zaka danna gurin da nace ka danna ma’ana Danna nan bayan ka danna kai tsaye zai kaikai playstore. A nan ne zakayi download na Application din

Kai tsaye zaka danna yanda akasa install nan take zaiyi install shikenan saika fara amfani dashi. Na tabbata gai burgeka.

KU dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

mungode ??

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!