Yanda ake hada PDF File a wayar Android

A shafin nan mun yi bayanin menene PDF tare da amfaninsa, da kuma yanda ake convert din web page zuwa PDF a wayar Android. A wancan bayanin mun nuna yanda zaka juya web page zuwa PDF File a waya. Sannan kuma copy na url din wancan page din za ka yi, sai ka dawo cikin wani application ka yi paste nasa, sannan ka saukar da wancan web page din a matsayin PDF.

Web page shafine daya daga cikin shafuka da suke kunshe a wani website ko blog. Kai da kake karanta bayanin nan, kana karantashi ne a daya daga cikin web page din da shafin nan ya kunsa. Hatta wannan tutorial din da kake karantawa za ka iya juya shi zuwa PDF, kaman yanda muka nuna a wancan bayanin da mu ka yi.

Kafin mu fara bayanin yanda akeyi, sai an tanadi kayan aiki wadanda ga su nan mun bada sunayensu tare da link din da za a saukar da su. Sai a tanadesu kafin a fara hada PDF a waya. Bayanin yanda akeyi yana kasa – sai ayi kasa a ci gaba da karatu.

Ga kayan aikin

  1. PDF creatorπŸ‘‡

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.dbd.pdfcreator&hl=en

  1. Adobe reader πŸ‘‡

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.adobe.reader

Adobe Reader application ne wanda ake amfani da shi a Android domin a karanta PDF. Shi kuma PDF Creator application ne wanda ake hada PDF da shi a Android. Sai ku yi kasa ku ci gaba da karatu – bayan kun tanadi kayan aikin da muka lissafo a sama.

Ga Yanda Akeyi

  1. Da farko, ku saukar da application mai suna PDF Creator a link din da mu ka bayar a sama. Bayan kun gama saukar dashi sai ku yi install nashi.
  2. Ku na gama install na application din, sai ku bude shi. Ku na budeshi za ku ga Images, da Browser, da Contacts, da Notes, da Clipboard sai kuma PDF Created daga karshe.
  3. Bayan kun bude application din, sai ku shiga Notes, ko Clipboard ku rubuta bayanin da kuke son rubutawa a cikin PDF din. Idan kun gama rubuta bayanin da za ku rubuta, sai ku duba daga can sama ta bangaren dama za ku ga wani farin zane mai kamada folda, sai ku tabashi.
  4. Ku na taba wancan zanen za ku ga ya kawo muku inda zaku rubuta sunan PDF din. Sai ku shiga inda aka rubuta Enter PDF File Name, ku rubuta sunan PDF din.
  5. Ku shiga wajen ku rubuta sunan file din, sai ku taba DONE. Kaman yanda kuke iya gani mun rubuta Sadarwar satellite shine sunan PDF din a hoton dake kasa.
  6. Kuna yin haka shikenan kun rubuta PDF File naku a cikin wayar Android.
  7. Idan kuna son ganin PDF din da kuka rubuta sai ku shiga PDF Created.
  8. Kuna shiga PDF Created za ku samu wannan PDF din da kuka hada.
  9. Kuna shiga wajen za ku samu PDF din da kuka rubuta – sai ku bude shi. Za ku ga PDF din ya bude dauke da rubutun da kuka yi.
  10. Idan kuna so ku gano PDF din da kuka hada a cikin memoryn wayarku, sai kuje kan memoryn wayoyinku za ku samu wasu sabin foldodi guda biyu wato PDF-Creator da PDF Files
  11. Sai ku shiga folda ta farkon wato PDF-Creator – kuna shiga za ku samu wannan PDF din a cikinta.
  12. Wadannan matakan za ka bi, idan kana bukatar hada PDF a cikin wayar Android. Wadannan matakan da muka nuna a sama sune matakai mafiya sauki wajen hada PDF, kuma da wayar Android akeyin komai.

PDF File ba a iya budeshi a waya ko computer sai anyi amfani da wani application ko wata software. Amma a yanzu wayoyi suna zuwa da application din da ake bude PDF a cikinsu – hakama computer ana samun softwaren da ake bude PDF dasu a cikin Windows nasu.

A sani wannan PDF din da muka hada karamin PDF ne, wato wanda rubutune kadai a cikinsa. Manyan PDF sune zaka samu cikinsu akwai hotuna domin mai karatu ya samu karin bayani akan rubutun da yake karantawa.

Za mu dakata anan muna godiya da kawo ziyara shafin nan. Da fatan zamu sake ganinku – kuna iya ajiye tambayoyinku a wajen comment dake kasa, zaku samu amsa idan Allah yasa mun san amsar tambayar. A huta lafiya!

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!