Abubuwa 5 masu mahimmanci ka sani game da GPT-3 da ChatGPT.

  1. GPT-3 wata babbar model ce na Artificial Intelligence da kamfanin OpenAI ya ƙirƙira domin samar da rubuce-rubuce kamar yanda mutane keyi. An gina ta ne akan wani tsari (architecture) da masu bincike daga kamfanin Google da Jami’ar Toronto suka samar a shekara ta 2017 me suna “Transformer”.
  2. ChatGPT kuma wani bangare (derivative) ne da’aka samar dashi daga GPT-3 a matsayin mutum-mutumi (chatbot) me iya bada amsoshi ga tambayoyi iri-iri.
  3. GPT-3 (da kuma ChatGPT) ba Artificial General Intelligence (AGI) bane amman wani yunƙuri ne na cimma AGI. AGI tawuce rabuce-rubuce kawai. Haryanzu ba’a cimma matsaya akan menene shi kansa “AGI” ba.
  4. GPT-3 (da ChatGPT) ba za ta maye gurbin Google bah. Google injin bincike ne (Search engine) ita kuma GPT-3 kimiyyar rubuce-rubuce ce da ake kira da Large Language Model (LLM). Wato manyan models wanda akayi su don fahimtar yarukan mutane.
  5. Ba GPT-3 (OpenAI) kaɗai ne LLM ba, akwai irinsu BERT (Google), T5 (Google), Roberta (Facebook), DeBERTa (Microsoft), da dai sauran su. Amma dai GPT-3 na daga cikin babba a cikin su.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!