yanda zaku mayar da hotanku kamar cartoon

Assalamu Alaikum yan uwa barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan sabon darasi a yau nazo muku da wani sabon Application mai matukar amfani wanda na tabbata zai burgeku. 

WANNAN WANI SABON APPLICATION NE 

Sunan wannan Application din Photo Lap wannan wani sabon App ne da aka kirkire shi a shekarar 2019 amma bai shahara ba ma’ana mutane basu sanshi ba App din ya fara tashe ne a shekarar 2021 lokacin da wasu daga cikin yan masana’artar knywood suka fara amfani dashi wajan mayar da hoton su tamkar cartoon suna dorawa a social media ma’ana kafafan sada zumunta wannan App ne dazai baka dama kayi editing din hoton ka ya koma tamkar Cartoon zakaga hoton yayi kyau sosai sannan zai burgeka.

A takaice dai wannan Application din zamu iya cewa yan masa’antar knywood ne suka tallata shi a duniya har ya samu kar buwa a wajan al’umma.

A shekarun baya kafin App din ya fara tashe ma’ana kafin asan shi wasu yan social media suna biyan kudi da tsada ana yimusu editing din hoton su da wannan Application din ya koma tamkar Cartoon domin su mai dashi LOGO na kasuwancin su kuma sana biyan kudin ne ga wanda suka san wannan Application din a baya domin su mayar musu da hoton su tamkar Cartoon.

zamu iya cewa wasu mutanen a baya sun samu kudi da wannan Application din dan haka wannan zai tabbatar muku da cewa wannan Application ne kyau kuma na tabbata idan kayi amfani dashi zakaga ya burgeka sosai.

YANDA ZAKAYI AMFANI DA WANNAN APPLICATION DIN 

Da farko kana shiga cikin Application din yana budewa zai fara kawo maka samfur na hotunan mutanen da suka mayar da hotunan su tamkar cartoon zakaga gansu kala daban daban sunyi kyau sosai ba’a cewa komai daga sama zakaga Application din yana da abubuwa guda uku abun na farko

TOP idan ka danna top zai kawoma samfur na hotunan maza da mata wanda wannan Application din ya mayar da hotunan tamkar cartoon abu na biyu

TRENDING shima Trending idan ka danna shima zai kawo samfur na hotunan maza da mata wanda wannan Application din ya mayar musu dashi tamkar cartoon abun ban sha’awa zakaga sunyi kyau sosai

RECENT haka shima recent zai kawo ma hotunan mutanen da wannan Application din ya mayar dasu tamkar Cartoon kamar yadda Trending da top suka mayar. 

A cikin Trending da Top da Recent idan ka shiga daya daga ciki idan kaga hoton wani wanda wanna Application din ya mayar da hoton sa tamkar cartoon ya burgeka kuma kana sha’awar kaima ka maida hotonka tamkar irin sa to kai tsaye zaka danna kan wannan hoton kana danna wa zai kawo ma hoton na asali da kuma hoton da Application din ya Chanjer shi ya koma tamkar Cartoon 

to daga nan Application din zai kara burgeka sabu da zakaga asalin hoton daka sa da hoton da wannan Application din ya mayar ma dashi tamkar Cartoon babu wata mara ba kamar an tsaga kara App din basa Chanjer wa mutum asalin kamanin sa

Daka kasa zakaga ya kawoma Gallery Camera tare da kawoma wasu daga cikin hotunan dake cikin wayarka idan ka buda a cikin hotunan babu hoton da kakeso ka Chanjer shi ya koma tamkar Cartoon zaka iya danna gallery ka dauko hoton da kakeso Application din ya mayar ma dashi tamkar Cartoon idan kuma a lokacin kakeson daukar hoton zaka iya danna Camera ka dauka cikin sauki.

Idan ka zabi hoton da kakeso wannan Application din su chanjer mashi ya koma tamkar Cartoon saika danna kansa ka shigo dashi cikin wannan Application din kana shigo dashi zai kawo bangaran da zaka saita hoton idan kana son rage masa fadi ko tsayi sai ka rage masa idan kuma hoton a kwance yake ko a kaikaice yake ka iya daidai tashi ya dawo nomal idan kagama saita shi saika danna aron dake kansan hoton kai tsaye zai hoton zai tafi (PROCESSING) yana gama wa zasu kawoma sun mayar ma da hotonka tamkar Cartoon idan kana son downloading din hoton ya koma cikin wayarka zaka danna digo digo guda uku na barin hannun damanka dake sama kana danna wa zai kawo ma (Save to devices) saika danna kana danna wa idan ka duba daka kasa zakaga inda akasa Download saika danna kai tsaye hoton zaiyi sevin a cikin wayarka.

ANIMATE 

Kafin kayi seving na hoton idan ka koma baya zakaga wata alamar plus ta bayyana daka kasan hoton saika danna ta kana danna ta zaka kawoma zabi guda uku saika inda akasa (ANIMATE) kana danna wa wannan bangaran zai baka dama ka maida hoton ka wani dan short video ta hanyar sa masa alamar Love mai motsi da dai sauran abubuwan mamaki.

IDAN KANA SON DOWNLOAD DINSA GA LINK NAN A KASA

https://play.google.com/store/apps/details?id=vsin.t16_funny_photo

kana danna wa zai kaikai playstore to anan ne zaka yi download na Application din.

Yana gama download kai tsaye Application din zai fara install da kansa yana gama wa App din zai sauka akan wayarka shikenan saika fara amfani dashi. 

KU dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha

mungode 🤝🤝🤝

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!