yanda zaku yi Kiran waya kauta( Free call)
Assalamu Alaikum yan uwa barkan mu da sake saduwa daku a wanan lokacin cikin wannan sabon darasi a yau nazo muku da wani sabon Application mai matukar amfani wanda zakai Free Call ma’ana kiran waya Kyauta.
WANNAN WANI SABON APPLICATION NE
Sunan wannan Application AbTalks Call wannan sabon Application zai baka dama kayi Free Call ma’ana kayi kiran waya Kyauta ba tare daka sa kati ba mun binciko muku wannan sabon App ne sabuda akwai lokacin da kake son kayi kiran waya kuma baka da kati gashi babu kudin sa katin ba fatan hakan muke ba to a wannan lokacin zaka iya amfani da wannan App din kayi kira kyauta.
YANDA AKE AMFANI DA WANNAN APPLICATION DIN
Da farko zaka shiga cikin Application din kana shiga idan ka duba daka kasa zakaga ya kawo ma zabika guda hudu bayan nan zakaga wata alamar zero daka tsakiya zaka danna ta kana danna wa zai kawo ma wajan da ake sa lambar waya idan za’ayi kira daga gefe zakaga County Code +234 na kashashe da yawa zaka danna ka zabi County Code na kasar ka idan kai dan Nigeria sai kasa Nigeria idan ba dan Nigeria bane saika danna kasar ka.
ABUBUWA HUDU DAKE CIKIN WANNAN APPLICATION DIN
CONTACT
Idan zakayi kira zaka danna Contact kana danna wa zai kawo ma dukkan nin lambobin dake cikin wayarka idan zakayi kira saika danna.
PURCHASE
zaka danna purchase idan kana so ka biya da yake Application din na kude amma akwai ban gare Free Call kana danna wa zai kawo idan zakayi Adding din Information na ATM CARD dinka saika biya.
Idan kuna son ayi muku cikakken bayanin yanda ake siyan kaya a Internet da ATM CARD kuyi comment a kasan wannan darasi.
POINS
wannan ban garen shine na Free Call wato kiran waya Kyauta zaka danna poins kana danna wa a nan ne zakayi ayyukan da zaka tara Poins wanda dashi zaka dinga Free Call.
YANDA AKE TARA POINS
kana shiga ban garen poins zakaga inda akasa Daily Check in shi daily check in poins wanda suke bayarwa kullum sau daya suna bada +100-700.
Daka sama zakaga dinga ganin adadin poins din da kake dashi.
Lucky Spain
shi kuma lucky spain zaka dinga danna shi a duk lokacin da kake bukata kana danna wa zasu baka poins adadin yanda sukaga dama.
Ta Wannan hanya zakabi ka tara poins wanda zaka dinga Free Call dashi.
DIAL
Wannan ban garen shine wajan da ake sa lambar waya idan za’ayi kira wato DIAL idan poins dinka yakai adadin da za’a iya free call dashi kana sa lambar da kake son kira zaka danna Call idan poins dinka yakai adadin zaka gani.
IDAN KANA SON DOWNLOAD DINSA
Kai tsaye zaka danna gurin da nace ka danna ma’ana Danna nan bayan ka danna kai tsaye zai kaikai playstore. A nan ne zakayi download na Application din.
Kai tsaye zaka danna yanda akasa install nan take zaiyi install shikenan saika fara amfani dashi. Na tabbata gai burgeka.
KU dai ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa kimiyya da fasaha
mungode