CUTUTTUKA 20 DA SHUWAKA KE MAGANINSU CIKIN YARDAN ALLAH
Cuttuka 20 da Shuwaka ke Warkarwa a jikin Dan Adam Insha Allah.
Ganyen Shuwaka wata ciyawa ce mai launin kore wacce ke girma a sassa daban-daban a Kasashen Nahiyar Afrika da ma Nahiyar Turai, har ya zuwa wasu yankuna na Kasashen Larabawa
Bincike ya nuna inganci da sirrin da ke tattare da wannan ganye, kama daga ganyenta, Saiwarta, da itaciyarta
Kabilar Igbo na amfani da ganyen su yi abinci musamman miya, su kuma Yarbawa sun dauki Shuwaka a matsayin magani wanda suka tarar kakanninsu na amfani da ita tun asali.
A Kasar Hausa kuma, Mata masu jego da masu shayarwa ne suka fi amfani da ita.
Mun yi amfani da wannan damar wajen binciko maganin da Shuwaka ke yi a jikin Dan-Adam.
Gasu kamar haka:
1 Bincike ya nuna cewa ganyen Shuwaka na wanke hanta daga kwayoyin Cuta, domin hanta ta kasance abu mafi nauyi a cikin jikin Dan-Adam. Zukar suga da kwankwadar giya da shan magunguna barkatai na illata hanta, wanda kusan duk abin da ya shafi hantar mutum to a hakika jiki zai fuskanci barazanar kamuwa da cutuka.
- Shuwaka na taimakawa koda sosai wajen karfafa aikinta, koda wata muhimmiyar halittace da ke aikin fitar da duk wasu abubuwa marasa amfani daga cikin jiki, kamar fitsari
3 Idan kana fama da yawan tunani to sai a tace shuwaka a sanya dan garin dabino kadan sai a zuba zuma a sha kofi daya a kowace rana, kwakwalwa za ta washe.
4 Shuwaka na maganin kasala marar misaltuwa, a nemi ganyen shuwaka a sabe a sha lita Daya da safe haka za a maimaita da yamma, a yi haka na tsawon wata daya
- Idan an ci wani abinci wanda ya lalata ciki to a sha ruwan shuwaka zai taimaka wajen daidaita lamuran jikin.
6 Gudawa ga yaran da ke shan nono a saboda rikicewar nonon sai uwar ta tace shuwaka ta sha a sanda za ta kwanta, haka idan gari ya waye za ta sha.
7 Shuwaka na wanke dattin ciki.
8 Tana maganin tsutsar ciki.
9 Duk wanda ke bahaya da kyar ko mai tauri ya dinga shan ruwan shuwaka.
10 Duk mai fama da rashin bacci ya dinga shan shuwaka.
11 Yana maganin Kumburin ciki da zafin ciki.
12 Shuwaka na maganain basir mai sa kumburin dubura.
13 Yana maganin zafin ciki ko kaga kana bayan gari amma hayaki na tashi a ciki.
14 Karin ruwan nono ga mata masu shayarwa a nan sai a rika yin kununta a na sha.
15 Tana tsaftace nonon da ya gurbace.
16 Tana warkar da Cututtukan fata sai a sabe ta a shafawa wajen da ke da matsalar.
17 Mai fama da cutar zazzabin cizon sauro ya dunga sha a na surace da ruwanta ko wanka da shi, amma da duminsa.
18 Tana kashe kwayoyin cuta.
19 Idan kana neman ka tsaftace cikinka daga yawan tugugi da tsuwa to sai ka gyara shuwaka ka sha.
20 Mata masu fama da matsalar rashin haihuwa to a ake amfani da shuwaka.
Allah Ya bada Lafiya Ya sa a dace Aamin.