ILLOLIN SHAN MAGANIN CIWON JIKI KULLUM :

Yau a kasarmu Najeriya shan magungunan dauke ciwo barkatai kamar su Ciwo takwas, cataflam, feldine , da sauransu , sadrox sun zama ruwan dare , wanima ko lafiyar sa kalaw amma kullum sai yasha maganin dauke ciwo .

GA KADAN DAGA CIKIN ILLOLIN HAKAN :

1- Heart Failure : Zuciya ta kasa harba jini zuwa sauran hanyoyin jini na sauran jikin mutum. To yawan shan maganin dauke ciwo yana kawo wannan matsalar.

2- Peptic Ulcer : wadannan magunguna suna daga cikin abubuwanda suke haddasa gyembon ciki (kurjin ciki) Yakan iya shafan hanji ko ciki wanda Hamsin visa Dari na yan najeriya suna fama da wannan matsalar yanzu haka.

3- Renal Failure : yakan kawo cutan koda, wanda koda zai kasa sarrafa duk wani abinda kasha ya tura zuwa mahallinsu shima wannan masalar Arba’in visa Dari na yan Najeriya Idan za amusu URINEANLYSIS za kaga suna tare da wannan matsalar.

4- Dangers to Children and Teenagers: wadannan magungunan yana da illa sosai ga yara kanana har yakan kaisu da matsalar kwakwalwa (hauka). diyawa daga cikin mata idan sunzo asibity ana tambayar su wanne magani kuka bashi a gida sai suce CIWO TAKWAS .

5- High blood pressure : Wassu daga cikinsu sukan saka jinin dan Adam Yahau.

6- Liver Problem : Wassu daga cikinsu sukan lalata hantar dan Adam .

GARGADI

Mafi yawan ciwon jiki ba cuta bace alamar wata cutace , sabida haka duk wanda yake fama da ciwon jiki yagarzaya zuwa asibity domin agane me ya haddasa ciwon jikin, kuma abashi magani daidai da ciwonsa.

Allah ya karamuna lafiya

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!