MAGANIN LAULAYIN CIKI

Laulayin ciki abu ne wanda yake zuwa bisa yanayin halittar da Allah ya yiwa matar.
Domin akwai bambanci a tsakanin su kansu matan, wata matar tafi wata shan wahala a lokacin laulayi.

Ga wasu magunguna nan a nema a hada, InshaAllah za a dace:

  • Ganyen Na’a-Na’a (Fresh ko busasshe mai kyau).
  • Lemon tsami.
  • Zuma mai kyau.
  • Citta da Kanumfari.

yadda za’a hada

Da farko amarya Zaki dafa ganyen Na’a-Na’a kamar cikin tafin hannu 2 a cikin ruwa kofi 3, a zuba citta da kanumfari daidai misali a dafa su tare.
Idan an sauke, an tace ruwan sai a zuba zuma gwargwadon yadda ake so, sannan a yanka lemon tsami guda biyu (me ulcer Rabi), a matse a cikin ruwan da aka dafa din sannan asa a flacks ana sha kadan kadan wuni daya a shanye za’a samu sauki.

AMFANIN SA A JIKI
Mai Juna biyun za ta samu qarfin jiki, za ta dena yawan zubar da yawu (Miyau) da hararwa (amai) kuma jaririn dake cikinta zai samu kaifin basira da kwakwalwa.

Mungode

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!