Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Sake nada Adeyeye A Matsayin Shugabar Hukumar NAFDAC

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sabunta nadin Farfesa Mojisola Adeyeye a matsayin babbar daraktar Hukumar Kula da ingamcin Abinci da Magunguna ta kasa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Juma’ar nan.

DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa An rubuta, “ an sake nada Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye a matsayin babbar daraktar @DGatNAFDAC a karo na biyu kuma na karshe na shekaru biyar. Ta tsaya a shedkwatar hukumar da ke Abuja don ganawa da wasu Daraktoci.”

Haka kuma, wani babban ma’aikacin hukumar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.

Ma’aikatan sun ce an sake nada Adeyeye a matsayin shugabar hukumar NAFDAC daga ranar 1 ga watan Disambar 2022.

Adeyeye, wacce aka nada a shekarar 2017, ta zo karshen wa’adin mulkinta na farko a ranar 2 ga watan Nuwambar 2022.

Jaridar Primetimenews ta rawaito cewa, Bayan cikar wa’adin farko na Adeyeye a matsayin DG, Darakta mai kula da rajistar miyagun kwayoyi da kula da harkokin hukumar ta NAFDAC, Dr. Monica Eimunjeze, ta karbi mukamin mukaddashin shugaban hukumar a ranar 12 ga watan Nuwambar 2022.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!