Yadda Zaka Fahimta Idan Anason Ayi Maka Hacking Na Account Dinka
Assalamu Alaikum Warahmatullah
Jama’a barkan mu da warhaka, Yau zamu yi bayani ne akan yadda mutum zai fahimta idan akwai wani ko wata da sukeson suyi hacking na account facebook dinka.
Kamar yadda kuka sani yanzu hacking ya zama to ruwan dare ko ina akwai hackers musamman na social media, amman duk da haka akwai wasu hanyoyi da dama wanda ake iya bi dan kare account dinka daga sharrin hackers.
Yau zamu yi bayani akan hanya ta farko da yakamata mutum ya bi dan kare kansa daga hackers,
Wannan hanyar shine zai taimakama mutum kafin wani ko wata suyi maka hacking account dinka, kamfanin Facebook da kansu zasu sanar da kai cewa akwai wanda yake son hacking account din ka, saboda haka sai ka dauki mataki na kara tsaro sosai a account dinka, sune zasu sanar da kai koda datan wayarka a kashe yake, ta inda zasu sanar da kai shine ta (Email da Phone number).
Karin Bayani: ta Number waya kadai za’a sanar da mutum idan data a rufe yake, na Email kuma sakon bazai shiga ba har sai lokacin daka bude datan wayarka.
Sunan wannan setting din da muke bayani akan sa shine (Unrecognized Login) Wannan setting din yanada matukar muhimmanci sosai, kowa yakamata ya tabbatarda ya kunna wannan setting.
YADDA AKE KUNNA SETTING DIN A FACEBOOK!.
Da farko zaka shiga Facebook dinka sannan saika danna alamar layi uku wato (Menu) daga nan kuma saika danna alamar (Settings) bayan haka saika nemi wurin (Security and Login) idan ka shiga wurin zaka ga (Get alerts about unrecognized logins) to anan kuma zaka ga (Notifications) da (Email) sai ka danna musu alamar (Edit) sannan sai ka saka (Namban wayarka) da (Username na Email dinka),
Bayan ka gama saita komai dai-dai shikenan duk lokacin da wani ya gwada Login account dinka Facebook zasu tura maka sakon cewar akwai wanda yake kokarin yin hacking account dinka.