Dalilan da suka sa aka ɗage training ɗin enumerators da supervisors A ƙananan hukumomi

zancen ɗage training na enumerators da Supervisors gaskiya ne, kuma ɗagewar yaza dole saboda wassu dalilai. Duka sa rana da ɗagewan yana fitowa ne daga mataki ƙasa, wato daga Abuja.
Yazama dole aɗage bada horon saboda wassu dalilai kamar haka:-

  1. FITAR DA SUNAYE:- Yayin zama na ƙarshe ajiya shugabannin Census na jihohi sun tabbatar wa shugaban na ƙasa cewa sunayen da suka fitar be fitar da sunayen duk Enumerators da Supervisors ba, kuma sun tabbatar cewa jihohi dayawa har yanzu yawan enumerators da Supervisors be Kai abunda ake bukata ba. Shugaban na ƙasa beji dadin bayanin nasu ba, hakan yasa yace kar a fara training har sai kowanne LGA ta cika adadin ma’aikatan ta kuma an fidda sunaye duka.
  2. CHANJA FASALIN YADDA AIKIN ZAI GUDANA:- Technical team sun tabbatar da cewa za’a samu matsala in har ba’a sauya fasalin aikin ba, a farko kowanne Enumerator zai irga EA daya ne shi kadai, yanzu kuma sunaso ahaɗa team of enumerators mutane 5 aciki mutum 4 su zama sunada PDA ahannunsu suna tattara bayanai mutum ɗaya kuma reserve, abisani zasu irga EA sama da ɗaya a tare daga wannan EA zuwa wancan, Arinƙa juyawa, me PDA ya koma reserve, reserve ya koma me PDA ahaka ahaka har agama dukkanin EAs din.
  3. RASHIN TSAYAYYUN AZUJUWA ( CLASSES) :- Masu kula da classes sun tabbatar cewa wassu azujuwan basuda kujeran zama wassu kuma ba’a gama samun izni daga masu makarantun ba.
  4. SAUYA ADADIN MALAMAI A KOWANE AJI :- A ƙa’ida anaso asamu malamai 3 ne a kowanne aji me dauke da mutane 40 amma adadin malaman bazai kaina, ana shawarin mai dasu 2 awassu azujuwan.

MATSAYA:- Daga ƙarshe An umurce su dasuje su shawo kan kowacce matsala cikin ƙanƙanin lokaci dan Asamu agudanar da bada horon. Duk lokacin da suka warware waɗannan matsalolin za’a fara training.

Shugaban ya nemi afuwan al’umma game da wannan jinkiri da ake samu🙏

Allah sa mudace.
Comrade Zuhairu Ibrahim
12/04/2023

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!