DALILAN DAKESA MATA KE GANIN FARIN RUWA YANA FITO MUSU KAFIN KO ZUWAN PERIOD DINSU

MEYASA MATA KE GANIN FARIN RUWA YANA FITO MUSU KAFIN KO BAYAN GANIN PERIOD DIN SU?

AKWAI MATSALA NE TATTARE DA HAKAN?

✓Normally mafi yawan mata suna samun fitowar farin ruwa a gabansu throughout menstrual circle dinsu.

✓Akalla mata dayawa suna ganin farin ruwa mai kauri ko salala, mara launi yana fito musu a kowace rana, adadin daya kai kimanin cikin shokalin shayi. Launin ruwan yana iya sauyawa daga farin madara, zuwa farin ruwa, ko kuma baki baki (brown).

✓Banbancin launin ruwan ko kaurin sa yana ta allaqa ne da hormonal changes na jikin ta a lokacin da yake fitowa.

✓Wannan fitan farin ruwa da mace take gani ta gaban ta kafin period dinta normal ne, babu matsala tattare da hakan. Process ne da ake kira “Leukorrhea” Wani lokacin yana iya kasance wa yellowish.

✓Hakan yana faruwa ne sbd yawan hormones “progesterone” dayake taruwa ajikin ta. A wannan gaban ana kiran yanayin da “luteal phase”

✓Wa’ennan hormones kamar su”progesterone” “oestrogen” “androgen” etc sauyin yanayin sune ajikin ta shike sawa tayi ta ganin “vaginal discharge” yana fito mata.

✓ Idan “estrogen” ne sukayi yawa ajikin ta a lokacin, se ruwan ya kasance fari fari, mai yauki

kuma ruwa ruwa.

✓ Idan kuma “progesterone” ne sukayi yawa ajikin ta, se ruwan ya kasance farin madara kuma mai kauri kauri.

✓Koma ya launin ruwan ya kasance, fari ne, ruwa ruwa ne, madara madara ne, yana da kauri ko akasin haka, muddin baya wari ko qarni, gaban mace baya zafi, kaikayi ko radadi, to wannan normal ne.

✓Aikin sa (ruwan) shine yayi flushing duk wani dattin vagina, wasu harmful germs, etc da kuma ya sa vagina ta zama moist all the time. Hakan yana nuna alamar the vagina and the

reproductive system is healthy and functional.

WASU LOKUTA NE ZAKI TSAMMANCI GANIN FARIN RUWA A GABANKI; IDAN KINGANI BA DAMUWA BANE

✓Normally mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowane bayan yankewar period dinsu. bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danqo yakan sake bullowa wanda zayyi kamar kwana 4 zuwa 5 Kafin ovulation, alama she ta eggs sun fara developing. ana kiran shi da “follicular phase” that means a lokacin ne “eggs” (for ovulation) suke kokarin girma.

✓Idan kuma lokacin ovulation yayi, ruwan se ya

canza daga mai danqo zuwa fari mai yauki kuma mara kauri (salala) haka. A wannan lokacin yana kara yawa sosai fiye da na kullum a da. Shi kuma ana kiran shi “egg white”.

Aikin sa shine ya taimaka wajen santsin sperm a vagina da cervix domin ya samu daman isowa kwai da yake jiransa for ovulation.

✓Sannan Mata dayawa suna amfani da ganin wannan ruwan a matsayin alama ta ovulation dinsu, hakan yana taimaka musu wajen samun ciki da wuri ko kuma kaura cewa yin cikin. Wannan process din shi ake kira da “natural family planning” ko “fertility awareness method”.

  1. ✓Idan ruwa ruwan ya kasance mara kauri (salala) to ana kyautata zaton shine “fertile” (i.e ciki zai iya shiga kenan in Kwan ya samu sperm). Sbd a lokacin kwan zai sauka zaman jira.
  2. ✓ Idan kuma ruwa ruwan ya kasance fari mai kauri to shi kuma shine “infertile” (wanda ko an sadu ciki bazai shiga ba) sbd kwan har ya riqa, karfin sa ya kare, yanzu sedai ya harziqa, se facewa.

✓To irin wannan ruwa ruwan mai kauri zaki cigaba da gani daga bayan ovulation har zuwa wani period din.

✓Daga bayan ovulation din zuwa wani period din, yawan fitowar ruwan zai na raguwa a hankali, yana zamowa mai kauri kuma mai danqo again, wani lokaci har zaki iya jinsa kamar wata gum ko glue.

✓On average dai, yana kaiwa irin kwana 11 zuwa 14. That is tsakanin ovulation dinki zuwa wani period dinki kenan.

✓Wasu lokuta kina iya ganinsa yellowish haka kafin period dinkin.

✓Idan mace taga wani irin brown discharge a bayan period dinta kuma, bayan jinin ya dauke, se ta sake ganin wani baki baki haka brown ya zo mata, to shi din yana kasance wa tsohuwar jini ne daya daskare bai samu daman fitowa ba last time. Shine yanzu yake kamo hanya.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button