MAGANIN MALERIA DA TYPOID FISABILILLAH

Tabbas al’amarin ciwon typoid da maleria ya zama ruwan dare ga Kuma naci ayi allurai asha magunguna Amma kaga abun sai a hankali.

Sabo da haka wannan Cibiyar taga ya dace ta bayar da gudun muwa ga masu wannan larurar domin Samun mafita cikin Sauki da Yardar Allah.

Dokar Maganin kada mutum yayi aiki dashi sai ya tabbatar da cewa ciwon typoid da maleria ne yake damun shi domin da yawa wasu suna fama da matsalar hanta ne sai su dinga yawaita Shan maganin tyepoid da maleria kwana kadan da sunsha ya dawo. Abun da yafi daidai shine yin gwajin tyepoid da maleria da Kuma hepatitis don sanin stand na Lafiyar ku.
Sannan mace Mai Ciki kada tayi amfani dashi muddin sabon Ciki ne sai akiyaye.

Idan Ansamu tabbacin Typhoid da maleria ne yake damun mutum sai asamu wadannan abubuwan Kamar haka;

  • Ganyen Gwanda guda biyu
  • Ganyen Turare/dogon yaro wato zait
  • Ganyen Lemu
  • Ganyen Rairai/Rai dore wato Sanga Sanga.
  • Bawon Abarba
  • Tagargade

Sai a hadasu a dafa tare.

Yanda Zaku Amfani da shi.

Babban mutum yasa glass cup bayan Yaci Abinci da Safe Sai Kuma da dare bayan Yaci Abinci Shima.

Yaro daga shekara 10 zuwa biyar 30 ml sau biyu a Rana. Daga shekaru biyar zuwa shekara Daya 15ml. Zasu Sha.

Allah yakara mana lafiya da zama lafiya ameeen.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button