Dama Ta Samu: Hukumar Society For Family Health Na Neman Sabbin Ma’aikata
Assalamu alaikum warahmatullah, barkanku da warhaka, a yau zamuyi muku bayanine akan ydda zaku samu aikin NGO wato Non-governmental Organization a karkashin hukumar society for family health.
Ga Takaitaccen Bayani Gameda Hukumar Society For Family Health
Society for Family Health na daya daga cikin manya-manyan hukumomi masu zaman kansu a wannan kasa ta Nigeria
Fitattun ‘yan nigeria ukune suka kafasu a shekarar 1985 farfesa Olikoye Ransome – Kuti , Justice Ifeyinwa Nzeako , Pharmacist Dahiru Wali da Phil Harvey.
Hukumar society for family health na daukar ma’aikata lokaci zuwa lokaci domin suyi aiki a karkashin wannan hukuma ta society for family health, sannan hukumar tana biyan albashi mai gwabi a duk karshen wata.
Tsare-tsaren Aikin Society For Family Health Sune
Jahar Kano itace wajen gudanar da aikin; duk mai sha’awa zai iya cikewa daga kowace jaha yaje zaune, saidai kuma wajen gudanar da aikin a jahar kano ne.
Sannan kuma aikin cikakken lokaci ne wato daga safe zuwa yamma.
Duk mai sha’awar cike wannan aiki na society for family health zai aika da CV dinshi ta wannan E-mail address din saremu@sfhnigeria.org