Ga wata muhimmiyar Sanarwa daga Hukumar Inec tare da Hukumar NCC

INEC za ta haɗa gwiwa da NCC wajen yaɗa sakamakon zaɓe kai-tsaye a 2023

A shirinta na ci gaba da yaɗa sakamakon zaɓe kai-tsaye ta intanet a babban zaɓe na 2023, hukumar zaɓe ta INEC a Najeriya ta ce za ta gana da hukumar sadarwa ta ƙasar a ranar Talata.

Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya faɗa wa editocin kafofin yaɗa labarai yayin wata ganawa a Legas cewa ganawar da za su yi za ta ƙunshi shugabannin kamfanonin sadarwa huɗu na Najeriya.

Ya ce INEC na haɗa kai da NCC ne don gano kyakkyawar hanyar yaɗa sakamakon a kowane lungu da saƙo na ƙasar a kan loƙaci.

NCC ce ke kula da dukkan harkokin sadarwa na Najeriya, wadda ke da ƙananan hukumomi a ƙarƙashinta.

Wasu daga cikin jam’iyyun siyasa sun soki INEC game da yaɗa sakamakon ta intanet amma ta ce “babu gudu babu ja da baya”.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!