Yanda Ake bude blog cikin sauki
Assalamu Alaikum Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya Allah yasa. A yau na kawo muku bayani cikakke yanda ake bude blog cikin sauki, samun blog na mallakan kai abune mai kyau saboda zaka iya rubuta koh taimakawa ta bangaren Da ka shahara wanda in kana da basira zaka iya samun yan wasu changi. Akwai wasu dandali da dama wanda suke bayar da dama wajen bude blog kyauta in kana neman mafi sauki wajen aiki a nawa shawaran ka fara aiki da wordpress.com ko kuma blogger.com. in kana da basira ko kuma ka shahara zaka iya zama daya daga cikin kwararu ta hanyan amfani da naka shafin. Blogger yana bayar da daman bude wajen rubutun ra’ayin kai wato blog amma yana da iyaka. Blogger yana daya daga cikin hanya dake taimakawa mutane wajen koyon yanda ake amfani da shafi na yanar gizo cikin sauki, na rubuta wannan bayaninne ga masu bukatan su koyi yanda ake amfani da blog da kuma matakan da zaka bi wajen budewa. Kafin na fara cikakken bayani akwai wasu yan abubuwa da ya kamata mu sani.
ABU NA FARKO
Blogspot yana daya daga cikin manyan shafuka da suke taimakawa wa yan koyo yanda ake aikin blog, Shi dai wannan kamfani wanda aka fi sani da blogger mallakar babban ma’aikatar nan na Google ne, yana bayar da dama wajen fara rubutun ra’ayin kai ta yanar gizo.
ABU NA BIYU
In manufarka shine samun kudi ta hanyar yanar gizo yana da kyau ka samar da kwararren blog naka mai zaman kansa wato personal hosting site wanda zamuyi bayanin sa nan gaba.
YANDA ZAKA BUDE WAJEN RUBUTUN KANKA BLOG
Dan samun wajen rubutun ra’ayinkai wato blog da fari zaka ziyarchi www.blogspot.com sai ka danna mabullin create blog
kayi logging ta hanyan amfani da email address naka wato gmail in baka da email zaka iya budewa kyauta ne.
Abu na fari zakaga zabin cewar ka bude ta hanyar amfani da ‘google plus profile’ sannan a gefensa zaka ga ‘limited blogspot profile’ I na bada shawaran kabude da google plus profile saboda ingancinsa. Muddin kayi logging sai ka danna’create new blog’ wanda zaka gansa a tsakiya shafin
SA WA SHAFI SUNA
Mataki na farko anan shine zabawa shafinka suna tare da zaban domain naka, sunan shafi shine asalin sunan da ka baiwa shafinka misali in na littatafan hausa ne sai ka basa da suna “hausa novels”, “novels” ko kuma “littatafan hausa” ya dan gana da son ra’ayinka wanda zaka iya canza a duk lokacin da bukatan hakan ya taso. ma’anar domain kuma shine addreshing da za,a same shafinka kai tsaye ka kiyaye amfani da sunanka yana da kyau ka zabi adireshi wa shafinka mai tsari wanda zai baiwa mutane saukin rikewa, shima zaka iya canzawa duk sa’in da hakan ya taso. Wasu lokutan mutum yakan zabi addreshing shafinsa amma ta bangaren blogger zai nuna ma alamar cewa wani yana dashi koh bazaka iya budewa dashi ba in hakan ya kasance sai ka canza abunda ka saka izuwa wani.
Sai ka zabi tsari wato “Design” wanda zaka iya canzasa daga baya saboda wanda suke zuwa dashi sam bashi da kyau sannan kuma ba tsari. In ka kamala cika abubuwan dana lissafo a baya sai ka latsa maballin “Create blog”
Yanzu ka bude shafinka (blog) na kanka amma baka kammala ba da saura, akwai wasu abubuwa da ya kamata ka saita dan ya baka saukin gudanar dashi. Yanzu kana shafinka (dashboard) zaka ga jerin abubuwa da ke hannun hagunka wanda zamuyi bayani a kansu.
Abu na farko na jerin jandawalin shine ‘post’ nan shine wajen da zaka sa sabon rubutu zaka iya sa sabon rubutunka ta hanyan latsa “post” na farko zai kaika izuwa ga wani shafi inda zaka ga wasu akwatuna guda biyu. Akwati na farko karami mai dauke da “post title” nan shine wajen da zaka sa sunan post naka misali ”Yanda Ake bude blog cikin sauki”, akwati na biyu wanda shine babba nan wajen shine inda zaka sa cikkaken bayanin abunda ka rubuta ko kake son rubutawa wanda aka fi sani da “Body Post” zai iya daukan yare daban daban wanda baida adadin harufa.
Bayan ka kamala sa title post naka da kuma body post naka a bangaren hannunka na dama akwai jerin jandawali mai dauke da “publish”, “save”, “Preview”, da kuma “close” a sama bayan ka tabbatar da cewar komai kasa daidai sai ka danna mabullin publish shine zai baka damar saka post naka duk wanda ya ziyarci shafinka zai ga abunda ka saka shi kuma save in kayi rubutu ko kana rubutu saboda wasu yan dalilai kana so ka dakatar sai zuwa wani lokacin ka cigaba sai ka danna mabullin save in har ka danna save kai kadai zaka iya ganin abunda ka rubuta wanda ba zai fito a shafinka ba, zaka kuma iya canzawa ko gyarawa, preview aikinsa shine yake bada damar kallon abunda ka rubuta kafin ka danna mabullin publish. Close wannan mabullin zaka iya amfani dashi ne san da lokacin da ka shiga bisa kuskure koh kuma ka fasa rubuta abunda kake so sai ka danna mabullin close zai baka damar komawa Shashi na farko ko wanda ya gabata.
POST FORM IMAGE
Na biyu shine “stats” a nan zaka ga adadin mutanen dasuke ziyartan shafinka ko wani rana sati da kuma wata gaba daya.
Na ukkun shine comments anan zaka ga duk wani tsokaci da akayi bisa post naka.
Earnings nan wajene da zakayi register na samun kudi a blog naka abun kula!! kada ka shiga nan sai ka san yanda akeyi saboda zasu iya kin amincewa da kai. Wanda zamuyi bayani a yan kwanaki masu zuwa.
campaigns yana daya daga cikin hanyoyin da ake samun kudi a blog sai de shi ya banbanta da earnings shi earnings za’ana tallata kayane a blog naka shi kuma campaigns yana aiki ne a lokacin da kake duba abu a google search.
Pages waje ne da zaka sa takatacciyar bayani game da kai da kuma manufar shafinka ba sai wayannan kadai ba zaka iya sa wasu abubuwa san ranka amma sai kasan yanda zaka kirasu zuwa fuskan shafinka ba sawa kadai kayi zaizo ba sai an kirasa. Sanaan iyakansa shine guda ashirin 20 baya zarce haka.
Layout wannan shine yanda shafinka yake ko aka zayyana sa
Template nan shine wajen da zaka iya daura sura wato design na blog in kana dashi.
Settings nan shine inda saitunan shafinka suke ya kunshi komai dake shafin.
Reading list anan zaka iya sa shafin wani dan samun damar karanta sabon post nasa ba tare da ka ziyarci shafinsa ba
Help nan shine wajen taimako in kana da wani matsala da kake fuskanta in kana fahimtar yaren turanci zaka iya samu a wajen.
Kafin ka fara rubuta abu a shafinka yana da kyau ka samu ayima designing na blog naka yanda zayyi kyau gani kada kayi amfani da wanda suke zuwa dashi saboda bashi da dadin sha’ani kwatakwata.