Gyaran Muhalli

Munyi bayanin hanyoyi daba daban da zaki kula da dukkanin sassan jikinki da suke bukatar kulawa ta musanman, wanda indai zakiyi amfani dasu zakiga amfaninsu sosai.

Amma ko da kin kasance mai tsafta da gyaran jiki, ace komai na jikinki a gyare yake indai bakya gyara muhallinki to kamar kinyi aikin banza ne saboda amfanin gyaran muhalli daya yake da na gyaran jiki.

KADAN DAGA CIKIN AMFANIN GYARAN MUBALLI:

  • Ke da kanki idan gidanki a tsaftace yake koina fes fes yana kamshi, babu wata kazanta zakiji farin ciki a zuciyarki.
  • Maigida zaiji dadin zama a gida, bazaijishaawar fita waje ba 
  • Yaranki zasukasance cikin walwala, sannan bazasui shaawar fita daga gidan ba balle suje yawon banza
  • Zakiji dadin yadda baqi zasuna zuwa gidanki suna yaba irin jindadin da kike a gidanki
  • Cututtuka basa zama a tsaftatacce muhalli

Sannan ko sanaa kike musanman na kayan abinci zakiyi ciniki dayawa indai gidanki a tsaftace yake.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!