HANYOYIN DA ZAKI GANE MASOYINKI NA GASKIYA

akwai hanyoyin da dama da Zaki iya fahimtar ko mijinki yana kaunar ki, amma Zan kawo kadan daga cikinsu.

Idan namiji yana sonki to Zaki ga yana mutunta ki tare da sanin kimar ki.

Idan namiji yana sonki, to Zaki iya canza dabi’unsa daga marasa kyau zuwa masu kyau.

Idan namiji yana sonki Zaki ga yana son zama tare da ke tare da jin dadin Hira dake.

Idan namiji yana sonki zai dinga shaukin ki kuma zai dinga gudun abinda zai bata miki rai.

namijin dake son ki koda yaushe zai dinga ganin kin dace da shi, ba zai dinga ganin yafi ki ba.

namijin idan yana sonki hakika zai kasance mai sakin suka tare da murmushi a Gare ki, zai dunga kallon fuskarki kuma ya dinga baki labari yana
nishadantar dake.

Idan so ya Kai so a zuciyar namiji da kansa Zaki ji maimaita miki cewa wance ina sonki.

namiji idan yana sonki zai dinga kishinki amma kuma ba wai irin kishin da zai takura ba.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!