KASANCE MAI YIWA MAI GIDANKI WANKA DOMIN HAKAN NA KARA SHAKUWA DA SOYAYYA

Wani magidanci yana da matarsa da yaransa mata guda hudu ya kara aure, amarya ta zo da sabuwar kissarta, idan gari ya waye sai ta shiga da miji bandaki (irin bandakin nan na tsakar gida) ta yi masa wanka, abun yana damun uwargida, domin idan ana yin wankannan har wake-wake amarya ke yi yaranta suna ji su yi ta dariya ana yiwa baba wanka, don haka da ta ga amarya ta dauko ruwan wanka za ta kora yaranta daki ta kunna rediyo, a haka har aka kwana bakwai.

Sai dai bayan Gogan na ka ya koma hannun uwargida sai ya ce magana ta gaskiya ya saba da wankan amarya don haka dole itama ta dinga yi masa wanka, uwargida ta ce yayi hakuri da wankan yara za ta ji ko da na sa, ya ce shifa dole sai an yi wankannan.

Da bala’i ya ki ci yaki cinyewa uwargida ta hakura ta fara yi masa wankan, amma sai ta kora yaranta daki ko waje, amma wani lokacin suna tsaka da wankan yara za su fito ko su dawo gidan, wani lokacin idan tana aiki ya shiga bandakin sai ya ta kwala mata kira, yaran su falla su je suce mata mama baba yana kiranki ki masa wanka.

Abun ya ishi uwargida ta ga yaranta na shirin samun matsala don haka ta rannan ta buga kasa tace wallahi ba za ta kara yi masa wanka ba, nan da nan gogan na ka ya nufi gurin mahaifin uwargida ya kai kara, ya gayawa mahaifinta amarya na masa wanka amma ita tace ba za ta yi masa ba, itama ta gayawa mahaifinta bandakin a tsakar gida ya ke duk sanda ake yin wankan yaranta suna ji domin dole da safe idan zai fita kasuwa ake masa.

Mahaifin Uwargida ya hau fada, cewar dole ta bi mijinta, ko shi ya samu damar yin wankannan yi masa za a yi, haka uwargida ta tafi gida tana kuka.
Washegari gogan ya shiga bandaki yana ta kwala mata kira ‘Ke Indo! kina ina Indo! yara suka fara kwala mata kira ‘Mama baba yana kiranki.’
Indo ta fito daga kitchen dauke da bokiti da ruwan zafi a ciki ta nufi bandaki da gaggawa, tana shiga bandaki ta kamfato ruwa a kofin wanka ta kwara masa a jikinsa.
Nan da nan Goganka ya mike a gigice yana fasa ihu yana fadin ‘Kin kona ni Indo, wayyo Indo kin kona ni.’ Ya yi hanyar waje a gigice ta riko shi da sauri tana fadin ‘Maigida babu wando a jikinka, wallahi gaggawa na ke na manta ban surka ba, don Allah ka yi hakuri.’

Tun daga ranar ya ce bai son wankan Indo na amarya ya ke so tunda muguwa ce ita, Indo ta yi murna da hakan, sai dai lokacin amarya cikinta ya tsufa wanka ya fara zame mata wahala, daga karshe ta ce itama ta gaji da wankan nan, aka yi ta rigima itama har da yaji, haka dai Goga ya hakura da wanka ya ce wallahi idan ya samu kudi sai ya kara aure ya samu mai masa wanka.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!