YADDA ZAKU FARA SAMUN KUDI A INTERNET ONLINE-KASHI NA (1)

MASU YAWAN YI MANA TAMBAYOYI AKAN HAKAN GA AMSAR KU.

Assalamu Alaikum ‘yan uwa barkan mu da wannan lokaci sannun mu kuma da sake saduwa daku a yau a wani sabon darasin mu na yadda mutum zai fara kasuwancin samun kudi ta hanyar amfani da internet, ko kuma nace yadda mutum zai fara samun kudi ta Online ta hanyar amfani da wayoyin hannun mu ko computers namu muna daga gida, kuma muna daga kwance nasan da dama mutanan mu sunason farayin haka wasu kuma suna yawon yi mana tambayoyi a kan hakan to insha Allah yau dai gamu dauke da duka amsoshin ku.

Kamar dai yadda aka sani Social Media wata kafa ce da take dauke da mutane daban-daban daga kowanne bangare na duniya, sai dai yanzu zamani ya sa social media sun koma hanyoyin samun aiki, dogaro da kai da kuma illimantarwa, matukar mutum zai dage ya kuma bada himma akan abun, kuma abin babu wahala matukar mutum zai bada lokacin sa ya tsaya yayi abin da gaske.

Wasu daga cikin hanyoyi ingattattu masu amfani da ake samun kudi a internet online ko kuma nace social media dasu sune zan bayyana su yanzu domin kusan su, kukuma san yadda ake amfanin dasu wajen fara samun kudi ta online, wato internet, wasu kuma zakuyi amfani dasu ne ta hanyar amfani da social media din ku dan samun kudi online, dan haka ga kadan daga hanyoyin da zan bayyana din:-

(1) Affiliate Marketing; Abinda ake nufi da affiliate marketing shine dillanci a social media ma’ana idan wani company yana siyar da kayayyaki ko services misali kamar online stores haka ko kuma wani company a online da suke siyar da wasu services ko kaya, zaka iya zama affiliate marketer dinsu idan zaku kulla yarjejeniya dasu zaka ringa hadasu ko kawo musu customers su kuma suna biyan ka, haka shi ake kira da affiliate marketing akwai kamfununnuwa da yawa da suke bada damar zama affilate marketer nasu a koda yaushe.

(2) Social Media/ Handle Manager; Zaka iya zama social media manager ta hanyar managing page din wani kamfanin ko wani celebrity ko dan siyasa ta hanyar kula da shafinsu kuma kana yi musu running ads ko da idan basu da lokaci, zakuyi yarjejeniya dasu suna biyan ka, wannan hanyar ana amfani da ita sosai musamman ga mutanen da basu da lokacin yin social media kamar ‘yan ball, yan siyasa, celebrities, kamfanunnuwa da dai sauransu.

(3) Influencing/Public figure; Wannan itama hanya ce mai sauki ta hanyar amfani da yawan mabiyanka ko followers naka a social media handles, a inda ‘yan kasuwa ko wasu suna baka tallar kayansu kai kuma kana musu talla a shafinka na social media irin wannan zakuga yawanci celebrities ko wanda a kasan suna da followers sosai ana basu talla suna sakawa a shafukansu ana biyansu wannan itama hanya ce ta dogaro da kai a social media.

(4) Blogging/Youtubing; Wanna kusan kowa yasan ta hanya ce dasu kansu google zasu na biyanka kudade masu yawa ta hanyar dora talla a cikin website din ka da kuma youtube channels din ka idan ka bude kana dora videos ko tutorials ko film da sauransu, idan website ne kuma ta hanyar saka labarai da sauran su, google zasu duba su baka adsence suna biyanka kudade in dollars.

Wannan sune wasu daga cikin hanyoyin da ake samun kudi a social media, ba iya su kadai bane kamar yadda kukaga mun rubuta a farko cewa wannan shine darasi Na Daya (1), Wanda a takaice dai muna nufin zamuna kawo muku hanyoyin samun kudi online daki-daki a duk lokacin da muka samu lokaci wannn shine darasi ma farko da muka Fara akan hakan.akwai hanyoyi da yawa sunanan,

Wadannan dai kadan ne daga cikin su nakawo mana wanda nake ganin kuma zaku iya zabar wanda kukaga zaku iya domin ku gwada, har Allah ya taimake mu gaba ki daya, ina fatan kowa ya fahimta kuma zamu amfana da kadan daga cikin wadannan hanyoyin.

Mungode sai kunjimu a darasi na gaba, Dan Allah kar a manta wajen yi mana share na duk darasin da aka karanta a wannan wabesite mai Albarka domin ‘yan uwa su shigo sugani suma su amfana, dan mu amfana baki dayan mu.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!