MENENE CYBER SECURITY?

Muna cikin wani zamani wanda ilimin kimiyya da Fasaha yake da tasiri matuqa a cikin rayuwarmu da Al’amurran mu na yau da kullu.

Kanfanoni ko qungiyoyi na Gwamnati da Masu zaman kansu, da al’umma masu yawa daga cikinmu wanda aqalla 80% na mutanen wannan zamani da suke amfani da yanar gizo muna ajiye sirrikanmu da Dukiyoyinmu harma da Takardunmu masu matuqar muhimmanci a Bankunan da muke ajiya ko akan YANAR GIZO ne wanda akafi sani da INTERNET.

Wasunmu sunayin ajiye ajiye na abinda ya shafi: Hoto, Lambobin waya, Saqonni, Sounds, Videos da sauran Files/Documents a Banki ko akan Google Drive, Email, I cloud, Facebook, Twitter, Instagram, dadai sauran kafafen sada zumunta na internet wanda kuma Wadannan Files/Documents Suna da mahimmanci matuqa a rayuwarmu wanda bazamuso ace wani ya mallakesu ba tare da yarda ko izininmu ba.

Zai yuyu a koda yaushe akwai mai bibiyarka/ki domin ganin ya samu wani sirri naka/ki wanda zai iya yin amfani dashi wajen ganin ya cuta maka/ki a rayuwarka/ki.

Ilimin CYBER SECURITY Ilimine wanda ya qunshi hanyoyi Daban-Daban wadanda suke wayar da kan Al’umma akan hanyoyin da zasubi domin ganin sun Kare Files/Documents nasu da suka dora a YANAR GIZO (INTERNET), Ko Suka ajiye a Banki, daga fadawa hannun mamuguntan mutane da zasu iyayin amfani da wadannan Files/Document ta wata Mummunar Hanya.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!