KIJI WANNAN DA KYAU ‘YAR UWA
Malama ki daina Bleaching! ki tsaya a matsayin da Ubangiji yake son Ganinki, karki manta Mazan da kike domin su Ubangiji ya Bambanta Ra’ayoyinsu kamar yadda ya Bambanta Halayensu, kowanne da kalar Wacce Yake so, Wani Baka (Black Beauty) Wani Fara yake So, Wani Gajeriya yake so, Wani Doguwa yake so, Wani Mai Kiba yake so, Wani kuma Siririya yake So, kowa da kalar Ra’ayinsa, kasancewarki Baqa yana da kyau kibar kanki a baqarki ba sai kin butulcewa Ubangiji bisa Ni’imar da yayi miki ba.