SANARWA GA DUK WANDA YASAN YA CIKA AIKIN KIDAYA

Muna sanar da jama’a cewa ranar talata 11 ga April 2023 ku ziyarci ofishin hukumar kidaya dake cikin karamar hukumar ku domin duba sunayen ku da ajin daukar darasi ,mun samu rahoto hukumar kidaya ta dakatar da turawa mutane sakon SMS ko Email address duk Applicant Status APPROVED ya ziyarci inda mukayi bayanin cikin rubutun nan zuwan yana da mutukar mahimmanci .

Hukumar Kidaya ta kasa ta aikawa dukkan Ƙananan hukumomi 774 sunayen mutane da aka aminci dasu don basu horo a ranar 13, ga April 2023 ku ziyarci ofishin hukumar kidaya ko ƙaramar hukumar ku domin duba sunan ku da ajin da zaku karbi horon, idan babu sunan ka zakuyi korafi ta hannun ma’aikata hukumar matakin ƙaramar hukumar ta hanyar karbar Nin number dinka da Npc in Sha Allahu mutukar an duba Application Status dinka yana Approval Kuma ka cike Enumerator ko Supervisor in Sha Allahu on 12 name dinka zai fito on 13 sai ka tafe wajen karbar horo .

Haka zalika mutanan da baa aminci da neman aikin su ba ma’ana APPLICATION Status Pending zasu iya ziyartar ofishin hukumar kidaya ko ƙaramar hukumar domin domin akwai Ƙananan hukumomin da har yanzu yawan ma’aikatan da ake bukata basu kai ba.

Ina yiwa kowa fatan alheri da samun nasara ,mu Sha ruwa lafiya .

©️Ahmed El-rufai Idris
Kaduna State Coordinator Zumunta Youth Awarenesses Forum.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!