SHAWARA GA YAN UWANA MATA MASU SON YIN AURE

بسم الله الرحمن الرحيم.

Yaku Yan uwana Mata masu daraja, ba komai yasa mafi yawa rubutuna yafi laqantuwa daku ba sai don kune cigaban wannan alummar, tabbas idan mata suka gyaru to alummar cikinsu ma ta gyaru, na san cewa aure abin so ne, kuma koyawa yana son aure, domin kuwa wani abu ne wanda Allah ya halicci kowane bawa dashi, mace tana son aure haka namiji yana so, idan kuwa mutum yace baya son aure ko shi aure bai dame sa ba to dayan biyu ne, kodai bashi da cikakkiyar lafiya ko kuma karya yake.

To amma akwai wadanda Allah ya jarabce su da son yin aure amman kuma abu ya gagara, wasu kuma suna fuskantar qalubale a soyayya da zamantakewar Aurensu. Nasan cewa da yawa sukan shiga damuwa musamman idan suka ga ƙannensu, ƙawayensu, sa’anninsu sunyi aure amma su ko manemi basu dashi kuma shekaru suna kuma tafiya, sai kaga idan babu ikhlasi da juriya sai mace ta fada halaka ta lalata kanta.

Wasu kuma suna da maneman suna son auren kuma da gaske suna da masu son aurensu, to amma kuma iyayensu sunki yarda ko basu goyon baya, wasu kuma sihiri akai musu, wasu kuma Allah yana son jarabtasu ne. To dai ko ma menene yar uwata karki manta cewa shi

Aure lokaci ne, kuma wasu haka Allah ya tsara musu zasu mutu basuyi ba.

Amman, yar uwata, kar kiyi tunanin cewa aure shine komai a rayuwarki ko kuma yin aure shine babban nasararki a rayuwa. Eh, gaskiyane cewa aure yana cika rabin addinin mutum to amman sauran rabin fa? Mai zai cika shi? Allah yasa kin fahimta? Amma bari na baki Misali :-

Ki kalli rayuwar Maryam (Allah ya kara mata yarda) Budurwace. Shin ta damu akan sai tayi aure? Shin ta tada hankalinta hurin bin malamai, bokaye, ɓatattu yan iska? A’a batayi ba hasalima sai ta ɓuge da yawan ibada da bautar Allah, ta gyara imaninta har Qur’ani ya bada misali da ita, kuma rashin aurenta bai sa taki zama shugabar aljanna ba, kuma da rashin aure aibu ne to da Qur’ani bai ambace ta ba.

Ki kalli rayuwar Khadija رضي الله عنها, ta kasance babbar yar kasuwa. Mai basira, hikima, ɗabi’a da daraja. Aikinta ko sana’arta bai tsayar da ita daga daukan matsayin mata ga Annabi ﷺ ba da matsayin uwa ga Zainab, Ruqayyah, Kulthum, da Fatimah. Kinga ashe ba iya aure ne rayuwa ba.

Duba Nana Aisha رضي الله عنها ta ruwaito hadisai 2,210 kuma kwararriyace a bangaren ilimummuka da yawa, mafi yawan sahabbai ma dalibanta ne. Kamar Qur’ani, Hadith or Fiqh. Mace mai hikimah, ilimi, basira, da wayewa. Ita ma Aurenta da Annabi ﷺ bai sa ta tsaya daga neman ilimi ba ko tace nauyin gida ya hanata karatu, hasalima babba ta zama cikin manya manyan maluman musulunci. ‘Yar uwa ke da baki samu daman yin auren ba mai kika yi a ilimi yanzu?

Yaku yan uwana mata, kun san matsayinku a matsayin ‘ya’ya, yan uwa, mata iyaye? Da ki tsaya tunanin yaushe zakiyi aure gwara ki tsaya ki gyara rayuwarki da lahirarki.

Ku nemi ilimi, ku koyar da Qur’ani, ki shiga islamiyya ki shiga neman ilimin addiniki ki ajiye tunanin yaushe zanyi aure? Ki sa tunanin yaushe zan zama kamar Nana Aisha? Ki zama abin kwatance cikin mata a gidanku, unguwarku, garinku da kasarki ma. Ki koyi sana’a, ki zama kwararriya a bangaren sana’arki, karki jira wai sai kinyi aure sannan zakiyi! Wallahi da ki tsaya ɓatawa kanki lokaci a banza wajen kallin fina finan india, soyayya, charts, fira, suyi ta saki mafarke mafarke, wallahi gwamma kiyi amfani da lokacinki wajen tara Qawayenki ko Qannenki ki zauna dasu kina basu ilimin da kike dashi ko yaya yake kuwa! Ke ko labarin annabawa ki karanta kina basu.

Wannan lokacin da kike zaune babu tsayayyen mijin aure, kiyi karatu ki karantar, wallahi rayuwa bata da tabbas! Yanzu sai ki ji ki acan. Kuma nawane suna wannan shekarun namu suka tafi? So kiyi koyi da matan sahabbai, ki san haramun, ki san halal, ki karanta ‘yan ci ‘ya mace a musulunci kiyi Qur’ani, ko a gidanku ki zama mai da’awa.

Yake ‘yar uwata ki tsaya kiyi amfani da kuruciyarki ta hanyar da ya dace, ta yadda zakiyi alfahri da tsufanki, kuma ki zama abin kwatance. Kiyi karatu kiyi sana’a. Yadda babu wani ɗa namiji da ya isa ya ɓude miki ido!

A ƙarshe yana da kyau ku sani cewa Shi aure lokaci ne, kuma idan Allah yayi zakiyi to zakiyi koda kuwa babu mazan dake kulaki, idan kuma dama cikin ilimin gaibunsa bai yi nufinki da yi ba wallahi duk wayon tara samarinki da binsu bazakiyi ba! Ki sani cewa ke ba wata madara bace da idan bakiyi aure da huri zakiyi expire ba!

Allah ka bamu ikon juriya da haquri mu ci jarabawarka a gare mu, kuma ka hadamu da masoya na kwarai

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!