Yadda Zakaga Hoton Ɓarawon Da Ya Sace Maka Wayarka Bayan Ya Saceta..
Rubutun zaiyi tsayi amma yanada matikar Amfani..
Nasan ƙila kuna gama karanta Heading na wannan rubutun zakuce; “Kamarya kuma naga hoton wanda ya sace min waya bayan kuma yatafi da wayar, ta wace wayar zanga hoton nasa, kuma tayaya..?
To kunsan yanzu lokaci ne na Technology duk abinda kake tunanin bazai yiwuba to a wajen kimiyya da fasaha mai sauƙi ne..
Daga lokacin da kasanya wayarka caji kokuma ka ajiyeta a ɗaki, sai kafita kofar gida kasha iska kokuma katafi yawo tare da abokai, sai shi kuma ɓarawon ya lallaɓo yazo ɗakinka yashiga ya ɗauke maka waya, yayi gaba da ita, To idan wayar taka tana cikin wannan tsarin da zanfaɗa maka yanzu to lallai zakaga hotonsa duk da ba wayar a hannunka…
Nasan tambayar da zakayi itace; ” Wai tayaya zanga hoton nasa ne??
To amsar itace: ta Email ɗinka, bayan ɓarawon ya sace wayar yatafi da ita, kasan matakin farko zaiso yacire wayar daga Security ɗin da kabarta, to da zaran yafara ƙoƙarin cire security na wayar, tunda baisan asalin security ɗin ba to yana sanyawa zata bashi “Wrong Password” to da zaran ta nuna mishi haka, zata ɗauki hotonsa zuwa Email naka.. zata ajiye maka shi acen, Kaga kenan duk wanda yayi trying cire security na wayar zata ɗauki hotonsa zuwa Email ɗinka, kana dawowa kaga babu wayar, to sai ka nemi wayar Abokinka kawai sai kayi login na Email ɗinka, kana hawa zata bayyanar maka da hoton ɓarawon idan har yayi attempting buɗe security ɗin.
Matakan da zakabi sune kamar haka: kai tsaye kaje Play Store ka ɗauko wannan App ɗin mai suna “App Lock-Finger Print” ka natsu sosai domin kasan akwai irin waɗannan apps ɗin waɗanda kuma ba duka suke aikin da akeso ba dan haka ita wannan App da zaka ɗauko zaka ga sunan kamfanin da sukayi ta a kasa shine; “Spsoft” Bayan kafara ɗauko shi zai iya nuna maka cewa yakamata kayi installing “Helper-(Applock), to kawai karka ɓata lokaci sai shima kayi installing nasa baya wani daɗewa zakaga shima yagama…