YADDA ZAKI FAHIMCI TSOHON SAURAYINKI YANA SONKI

Akwai wasu mazan da suke cewa sun rabu da mace saboda wasu dalilai. Amma a zahiri abun ba haka yake ba. Hankalinsu da tunaninu kaf ya kan wannan macen da suka yi ikirarin sun daina soyayya da ita.

Ga wasu alamun da suke nuna cewa namijin dayace miki ya daina kulaki har gobe yana sonki.

Idan kika ga tsohon mijinki ko saurayinki yana yawan tuntubarki ta waya, ko aika miki sakonnin gaisuwa ta hanyar wandanda suka sanki. Har yanzu yana sonki.

Haka nan idan kika ga tsohon saurayinki ko mijinki yana yawan son ya jawoki a jikinsa ko ya rika miki wasu abubuwa na kyautatawa. Hajiya har yanzu yana sonki.

Kishi yana daya daga cikin hanyar da zaki gane tsohon saurayinki ko mijinki na sonki.
Domin bai son yaji kina soyayya da wani, bazai so jin zakiyi aure ba.

Idan kikaga abokai da ‘yan uwan tsohon mijinki ko saurayinki suna sonki. Da Alamu cewa zuciyasa na tare dake.

Zaka kiga tsohon saurayinki ya kasa yin wata budurwa. Ko tsohon mijinki ya kasa yin wani auren ko kara wata matar bayan sakinki. Kina ransa.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!