ABINCIN DA MAI CIKI YAKAMATA TA RINKA CI

GUZURIN JIKI

Abinda gangar jikinta yake bukata sune kamar haka :

Hutu tare da kwancyar hankali.

Ta yawaita cin ganye (Kayan lambu) da kuma ‘Ya’yan itace.

Ta rika motsa jiki lokaci lokaci domin jinin jikinta ya rika zagawa sosai.

Ta rika shan shayin ganyen Na’a-Na’a domin samar da Qarfin jiki da kuma Kaifin basira ga jaririnta.

Ta rika amfani da Zuma domin samar da kuzari da kuma riga-kafi gareta da kuma jaririnta daga chututtuka.

Idan lokacin haihuwarta ya kusanto ta nemi dabino danye nunanne (irin wanda ake kira Siki) ta rika yawan cinsa. Idan bata sameshi ba, oda busashen ne ta rika amfani dashi.

Shan dafaffiyar garin hulba shima yakan yi amfani ga masu tsohon ciki. Yakan bama mahaifar Mace karfin turowa jaririn idan lokacin fitarsa yayi.

Ki rika shafa Man Tafarnuwa ko man Jirjir ko man Habbatus sauda domin magance ciwon Qafa din.

Wadannan duk ba zasu chutar da mai ciki ba. Koda shansu akayi.

Amfanin da shan rake ya ke yi wa mace mai ciki, da wasu 9

Duk inda ka hadu da gungun mutane suna zaune ana ta yada zantuka ba birki, sannan baki kuma na ta motsawa, to ina tabbatar maka cewa ana shan rake a wannan wuri.
Ko da yake sau da yawa, akan dan daga wa mai shan rake kafa a bashi uzuri saboda ganin yakan shiga wani hali na zautuwa idan ba a taro shi ba musamman idan anyi dace da raken mai zakin gaske.
Sai dai kuma wani hanzarin ba gudu ba, rake na da matukar amfani a jikin mutum wanda da yawa ba su sani ba.
Ga amfanin da rake take yi a jikin mutum.

  1. Rake na kara karfin kashi domin tana dauke da sinadarin ‘Carbohydrates’.
  2. Rake na dauke da sinadarin ‘Vitamin A’ wanda ke kara karfin ido.
  3. Shan rake na kare mutum daga kamuwa da zazzabi musamman idan aka matso ruwan aka sha.
  4. Rake na hana lalacewan kumba,karyewa ko canza kala.
  5. Rake na sa rauni ya warke da wuri.
  6. Yana kuma taimakawa wajen samun kaifin kwakwalwa.
  7. Shan ruwan rake na taimakawa wajen kawar da warin baki da lalacewar hakora
  8. Shan rake na kwara da matsalar rashin haihuwa ga matan da ke fama da wannan matsalar, yana kuma bunkasa girman jinjiri a cikin uwar sa sannan yana hana mata masu ciki yin bari.
  9. Rake na taimaka wajen hana jiki ya nuna tsufa da wuri.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!