KO KUNSAN AMFANIN APPLE A JIKIN DAN ADAM MUSAMMAN MATA MASU CIKI

wani sabon nazarin da manazarta na kasar Amurka suka yi, an ce, yawan cin apple da ayaba da kuma lemon zaki Na bada taimako wajen rage hadarin kamuwa da cutar gushewar hankali na tsoffi da kuma bawa Macce Mai Ciki dama wajen Samun Sauqin Haifuwa haka kuma yana saita ciwon zuciya.

Manazartan na jami’ar Cornell ta kasar Amurka sun bayar da rahoton, cewa lokacin da suke yin nazari kan amfanin da ruwan apple da ayaba da lemon zaki ke bayarwa kan kwayoyin jijiya, sun
gano cewa, sinadarin polyphenol da ke cikin wadannan ‘ya’yan itatuwa suna iya hana toshewar hanyar jini, da kuma ba da kariya ga kwayoyin jijiyoyi daga mummunan sinadari masu guba.
Ban da wannan kuma nazarin ya gano cewa, a cikin wadannan ‘ya’yan itatuwa iri uku, an fi
samun yawan sinadarin polyphenol a cikin apple, bayansa kuma sai ayaba sannan lemon zaki.
Manazarta suna ganin cewa, idan mutane suka kara cin wadannan ‘ya’yan itatuwa, to za a iya ba da taimako wajen yin rigakafin cutar gushewar hankali na tsoffi da kuma bawa Mata masu ciki damar haihuwa cikin sauki.
Ga dai Wani taimako da Ruwan Apple Suke bayarwa a jikin ‘yan Adam.

Suna saukar da Hawan Jini.
Suna saurin saka Rauni ya yi saurin warkewa.
Suna Maganin Warin Jiki, da warin hamatta.
Suna saka fatar mutum tayi kyau kuma tayi sumul.
Suna Maganin Warin baki, koda kuwa warin Na amosani ne.
Sunan karawa idanuwan Mutum gani, kuma suna saka ido fari.
Suna Maganin Fungal/Bacteria da kuma virus.

Godiya Ga Allah da Yayi Mana kayan marmari domin muci muji dadi kuma mu samu Lafiya a jikinmu.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!