ALAMOMIN CIWON KODA DA YADDA ZAKU KARE KANKU DAGA KAMUWA DA CUTAR

Alamomin da za’a gane koda ta fara samun matsala:

Masana harkar lafiya sun bayyana cewar koshin lafiyar koda na daga cikin sirrukan dadewa a duniya ba tare da gajiyawar jiki ba,

Koda na taka muhimmiyar rawa wajen tace wa da cire sinadarai ma su guba daga abubuwan da mutum ya sha. Koda na da alaka da sarrafa yanayin jinin jikin ta mutum,

Bisa la’akari da muhimmanci koda a jikin mutum ne yasa muka bunciko muku wasu daga cikin alamomi 7 da ke nuna cewar koda ta samu matsala, kamar yadda masana su ka tabbatar.

  1. Kumburi da taruwar ruwa a sassan jiki: Daya daga cikin alamomi na sahun farko da ke nuna cewar koda ta fara samun matsala akwai taruwar ruwa a cikin jiki da ke haifar da kumburi. Sassan jiki da wannan matsala ta fi bayyana su ne; kafa, hannaye, kafafu, ciki, da fuska.
  2. Sukurkucewar mafitsara: Yayin da mutun ya fuskanci ba ya iya rike fitsari kamar yadda ya saba a baya, ya gaggauta zuwa asibiti domin gudanar da bincike a kan yanayin aikin kodar sa.
  3. Gagarumin canji a launin fitsari: Launi, kala, da zarnin fitsari na daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen fahimtar aikin koda.

Idan fitsari yana kumfa ko tsananin zarni ko wari ko mutum ya ke jin zafi yayin fitar fitsari ko ganin jini a fitsari alamu ne da ke nuni cewar aikin koda ba ya tafiya yadda ya kamata.

  1. Kuraje a fata: Duk da akwai abubuwa da yawa da kan iya haddasa fitowar kuraje a jikin mutum, gazawar koda wajen tace wasu sinadarai ma su guba kan iya haddasa fesowar kuraje a jiki.
  2. Hawan jini: Masana lafiya sun bawa ma su matsalar koda shawarar su ke yawan ziyarar asibiti domin duba yanayin jininsu, saboda koda na taka rawa wajen daidaita sinadaran fatashiyom da sodiyom, sindaran da ke da alhakin da alhakin daidaita yanayin jini a jiki.
  3. Yawan gajiya da kasala: Yayin da koda ta fara samun matsala, mutum kan tsinci kansa cikin yawan samun kasalar jiki da gajiya, wasu lokutan mutum har jiri ya kan ji da rashin samun natsuwa.

YADDA ZAKU KARE KANKU DAGA CIWAN KODA KIDNEY

Daure ku karanta har karshe..

Aikata wadannan dabi’un marasa kyau ga mutum na iya jawo mai ciwon koda (Nephritis) don haka inkaji ko kinji wani Abu da kinsan halinka ne to ka daina.

1] RIKON FITSARI
Jinkiri wajen yin fitsari cutar da Kaine mutum ya kasance yanajin fitsari amma yaki zuwa yayi yaita rikon sa yana takurewa, to ku Sani duk sanda koda ta tace fitsari ta turo shi ga mafitsara ba abunda da akeso irin afitar dashi domin inkana rikeshi to ahankali wani zai fara komawa ga koda (kidney) wanda daga nan kuma matsala zata fara afkuwa.

2] KIN SHAN ISASHSHEN RUWA
Rashin shan ruwa wadatacce yadda ya kamata nan ma matsala ne yazama mutum yana jin kishi sai yasha kadan ko kuwa ma mutum ya gama cin abinci musamman mai maiko amma yaki shan ruwan kwata-kwata haka musamman abinci mai nauyi da mai Gina jiki irinsu (carbohydrate & protein). Mai irin wannan hali ya Kuka da kansa shi ruwa anso kake shan sa basai in kana jin kishi ba
Sannan inda hali in abinci ka gama ci to kasha ruwan mai dumi, kona tea ba ruwan sanyi ba. Inko na sanyi ne toh saika gama cin abincin da kamar minti 10 tukun

3] YAWAN SHAN GISHIRI
Yawan shan gishiri akwai matsala ga koda basai ga mai hawan jini ba, musamman mutanen dake da irin dabi’ar nan ta karama abinci ko Miya danyen gishiri idan bai musu daidai ba, to suma su kiyaye yana interfering da aikin cortex cikin koda.

4)] SHAN MAGUNGUNA
Rashin daukar kananun cututtka ko symptoms da mahimmanci wanda mutum ke ganin ko ba’a sha magani ba xa’a warke kamar jin zafin kuibin cikin wajen gadon baya ko murdawar ciki, zafin fitsari ko kaikayin makogoro ko ciwon mara yayin alada. Ta yadda mutum shine likitan kansa saide yaita dannawa jikinsa su paracetamol da feldin daka.

Sannan kuma shan magungunan ba bisa kaida ba, kuma ba yadda likita ya tsara ba, da kuma wanda dama ba likitan bane yasa wato (self medication) wannan na cutar da koda kwarai da gaske

Akiyaye please

Please share after reading

Don’t edit don Allah

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!