AMFANI 8 DA GAWAYI ZAI IYA YIWA LAFIYARKU DA MUHALLIN KU.

Gawayi bakin gawayina daga cikin abubuwan da aka fi wulakantar a gidajen mu. Jama’a da dama sun dauka amfanin gawayi ya tsaya ga girki ne kawai.
Sai dai gawayi na da amfani da yawa wajen inganta lafiyar jiki da tsaftace muhalli da mutane da yawa basu sani ba.

  • GAWAYI na Korar wari ko gyara gurbacewar iska
  • Shin takalmin ka sahu ciki na damunka da wari ko wani wuri a muhallin ku na yin wari? Saka gawayi cikin takalmi, firinji ko a daki zai yi maganin wannan matsala
  • Gawayi na maganin warin jiki idan aka goga shi baya an kwaba
  • Hana ‘ya’yan itace da ganye lalacewa
  • Ga duk mai son kar kayan miya, ganye ko ‘ya’yan itace su lalace sai ya saka su a cikin ruwan mai dauke da gawayi
  • Hasken hakora
  • Ga duk mai son hakoransa su yi haske sai ya daka gawayi sannan ya sami icen agada yake dangwala yana goge hakorama ko kuma ya daka gawayi ya hada da gishiri yake wanke hakoransa
  • Maganin tsamin miya
  • Shin kuna damuwa idan miyar ku ta lalace? Karshen damuwar ku ya zo. A mayar da duk miyar da tayi tsami kan wuta sai a dan saka gawayi daidai misali idan ta fara zafi. Gawayin zai cire dukkan tsamin da miyar tayi tare da dawo da dandanonta na asali.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!