AMFANIN GANYEN LANSUR A JIKIN DAN ADAM
Ganyen lansur nada matukar
mahimmanci a jikin mutum
domin yana warkar da cututtuka da dama a
jikin mutum. Akan hada ganyen lansur a cikin
abinci kamar shinkafa, faten
dankali, faten tsaki da kuma sauran
su domin taimaka wa jiki da lafiyar
mutum amma wasu masanan
ganyen sun ce ganyan ya fi amfani a jikin mutum idan aka ci shi danye,
wato a kwada shi ko da dakakken
kuli-kuli da kayan miya. Masanan ganyen sun bayana irin
amfanin da wannan ganye na lansur
ke yi a jikin mutum kamar haka
- Ganyan lansir na maganin cutar
- ido: Lansuru na da sanadarin dake
- maganin cututtukar da ke kama ido.
- Cin shi na da matukar Amfani
- Yana maganin cutar hawan jini
- Cin ganyen lansur na gyara fatar
- mutum. Lansuru na maganin Kyasfi
- dake kama fata. Ana nika shi a hada
- da man da ake shafawa ko kuma da
- ruwa a shafa a jiki. Yana gyara fata
- sosai
- Yana taimaka wa mutum cin
- abinci yadda ya kamata
- Yana maganin ciwon ciki kamar
- su zawo da sauransu
- Ganyen na kawar da ciwon
- zuciya
- Yana hana amai. Idan mutum
- yana yawan jin amai, lansuru na
- maganin shi
- Yana kara karfin kashi
- Yana kara karfin namiji
- Cin Ganyen lafsur na kawar da
- warin baki
- Cin ganyen Lansuru na kawar da
- laulayin da mata kan ji idan suna
- jinin al’ada
- Yana rage kiba a jiki
- Yana warkar da rauni ko ciwo a
- jikin mutum
- Yana kawar da cutar siga
- Yana kara jini musamman akwadashi asaka tumatur da Kuli aci
Allah yabamu dacewa