YADDA AKE HADA MAGANIN RAGE TUMBI, SANYI DA WANKIN CIKI
Yanda zaki hada maganin Tumbi, wankin ciki da infection lokaci daya
Abubuwan da za a nema
- Tsamiya rabin loka
- Ganyen Gwaiba 20
- Citta danye manya 2
- Lemon tsami manya uku
- Kurkum cokali daya
- Zuma
Yanda za a hada;
Ki daddaka citta, lemon ki wanke ki yayyanka ki matse ruwan a ciki kuma ki tsumbula har da bawon, ki wanke ganyen gwaiba sai ki hada su duka da sauran kayan ki dafesu idan ya huce ki murje tsamiyan ki tace su ki zuba Zuma yanda zai kashe duka tsamin ki rinqa shansa kamar juice din tsamiya zai wanko miki ciki ya rage tumbi ya kashe infections sosai da sosai.
Allah Ya sa a dace, idan kin karanta ki tura ma wasu