AMFANIN GANYEN TAFASA ( senna leaves ) DA ‘YA’YANTA GA LAFIYAR DAN ADAM.
Ana amfani da ganye da ‘ya’yan don yin magani. Tafasa maganin laxative ne da FDA ta amince da shi. Ana amfani da shi don magance Ulcer da kuma Cushewar da Ciki Ana kuma amfani da Tafasa ( Senna ) don maganin ciwon Ciki (IBS), ciwon basir, da Rage Kiba.
shayin Tafasa yana dauke da anthraquinone, wanda aka sani da tasirin laxative mai ƙarfi. Wadannan anthraquinone kuma Yana da tasiri sosai a tsaftace hanji, wanda yake da kyau ba kawai don ba da tsarin narkewa Abinci Ba, amma har ma da shirya hanji don hanyoyin kamar colonoscopy.
Tafasa wacce muka sani a kasar Hausa wata karamar bishiya ce dake da ganye launin kore da fure da kananin ‘ya’ya a jikinta.
Ita dai wannan bishiyar ana samunta a wurare da dama a kasashen Africa ciki harda Nigeria musamman a jihohin arewa.
A kasar India masu maganin Ayurvedic Herbal Medicines sun dauki lokaci mai tsawo suna amfani da tafasa dan yin maganin wasu kebabbun rashin lafiyoyi kamar haka :
Maganin makanta ko matsalar data shafi ta gani. A baya ga wannan matsala ta barazanar makanta, tafasa na kara lafiyar ido kama daga Yara har zuwa tsofaffi.
A dan haka sai a juri yin miyar tafasa ana ci a abinci.
Wani bincike da wasu masana tsirran itatuwa suka yi sun tabbatar da cewa Tafasa na maganin wasu cutukan da ke shafuwar babbar hanzanya (colon) da kuma taurin bahaya (constipation).
Tafasa tana maganin zafin ciki (internal heat) da kuma wanke dattin ciki da ya cushe.
Tafasa tana rage kiba dan haka wannan wata damace ga masu tumbi wadanda ke bukatar rage nauyi. sai a nemi ganyen tafasa a dake a tare da gero ayi Fura a Sha.
Ana amfani da saiwar tafasa idan suka bushe sai a dake su koma gari dan maganin cizon maciji.
Ana amfani da garin ganyen tafasa dan warkar da gyambon ciki wato ulcers.
Tafasa na maganin tsutsotsin ciki (intestinal worms)
tafasa na maganin cutukan fata kamar su kazuwa da makero da kuraje masu kaikayi ga jiki.
Please share after reading
Don’t edit don Allah