Amfanin Lemun tsami ga mata

Amfanin Lemun tsami ga mata

Dukanmu mukan yi amfani da lemo sau da yawa, amma yawancin mu ba ma san ainihin Amfanin sa ba musanman ga mata. Ana iya amfani da lemon tsami a kicin, amma ba iya nan amfanin sa ke tsayawa ba. Kamar yadda wataƙila kun riga kuka sani, lemun tsami yana ɗauke da sinadaran bitamin B da C, da calcium, potassium, magnesium da phosphorus. Wanda suke da kyau ga lafiyar mu
Lemun tsami na iya inganta jiki, magancewa da hana kamuwa da cuta, yana ƙarfafa tsarin garkuwar jikin mu har ma da rage yawan nauyi. Ana iya amfani da su ta hanyoyi daban-daban, amma a cikin rubutun yau, zan nuna muku yadda ake amfani da su don magance wasu matsalolin
Anan akwai hanyoyi guda 3 da akeamfani da Lemon tsami wanda yakamata mace ta sani kamar haka.

YANA SANYA FATA TAYI KYAU DA LAUSHI
Shafa ruwan Lemon Tsami yayin kwanciyar bacci kansa ya fatar jikin ki tayi kyalli da laushi, da kuma kashe wasu kwayoyin cututtukan da ke a jikin fata
YANA HASKAKA GASHIN KU
Kusamu ruwan Lemon tsami ku shafa a gashin kanku sauki barshi ya bushe zuwa wani dan lokaci sai a wanke da ruwan ɗumi, zai sanya gashin kanku kyalli kana yayi baki da tsawo kuma ya kashe muku ƙaiƙayin gashin kai
YANA KAWAR DA TABO AKAN FATA
Sanya ruwan Lemon Tsami akan tabo dake jiki kan kawar da duk wani tabo dake jikin ki, kawai a samu auduga sai a dangwali ruwan Lemon Tsami a goga a inda tabon yake. Insha allahu za aga abin mamaki

Allah yasa mudace

.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!