WANI MATSAFINE BAYAN YA TUBA YAKE BADA WANI LABARI MAI MATUKAR TADA HANKALI

Ga kadan daga cikin abinda yake fada;

“Na kasance a lokacin da nake ayyukan tsafe-tsafe mutane sukan zo daga kusa da nesa domin inyi musu mummunan aiki (irin wanda ake kira GOBE DA NISA).

Nakan tura aljanu su shiga jikin duk wanda aka sanyani inyi aiki akansa (Ko jinya ko kashewa ko raba tsakanin mutane ko mallakar miji, ko watsa arzikin wani) To amma akwai mutanen da idan na tura aljanu garesu nan take bukata take biya.

Akwai kuma wanda idan anyi aikin sai aljanun su dawo suce mun sunje wajen zamansa, ko gidansa, suna jin muryarsa amma basu ganinsa.

Wani kuma idan aljanun sunje gareshi sai su dawo suce mun “Muna hangensa daga nesa amma idan mun matso kusa sai mu dena ganinsa”.

Amma akwai kuma wadanda idan ya tura musu aljanu, sai Aljanun su dawo suce masa “Wallahi sun duba ko ina basu sameshi ba. Daga nan sai ya tura musu aljanu Maridai (JINNUL MARID sune mafiya taurin kai a cikin aljanu) amma su dinma haka zasu je su karaci neman su dawo basu ga mutumin da aka tara su wajensa ba.

Daga nan sai ya zabo Aljanu Ifritai ya turasu (JINNUL AFAREET sune mafiya karfin jiki da girman halitta a cikin aljanu) sai su dawo suce masa “Wallahi mun duba tun daga mahudar rana da mafadarta amma bamu ga mutumin nan ba.

Yakan tambayesu yace “Me yasa zaku ce baku ganshi ba, alhali yanzu haka yana nan a gidansa ko a shagonsa ko a wajen aikinsa?”

Sai suce “Wallahi mun duba fiye da sau dubu amma bamu ganshi ba”.

Wannan Boka matsafi yace “Yanzu bayan na tuba sai na fahimci cewar lallai mutane suna da bambanci da junansu ne bisa gwargwadon yadda suke kulawa da zikirin Allah da karatun Alkur’ani.

Akwai mutumin da kwata kwata babu ruwansa da zama da alwala ballantana azkar din safe da yamma. Sallar ma ba kula yake da ita sosai ba. To wannan shine wanda da zarar anyi masa sihiri yake kamashi nan take.

Akwai kuma wanda yakan yi azkar din lokaci lokaci amma yana da Qusuri (wato takaitawa) wajen yawaita karatun Alkur’ani ko nafilfilin dare. To irin wannan shine wanda idan shaidanun sunje gareshi zasu rika jin sautinsa amma sa ganinsa.

To akwai kuma wanda bayan yayi azkar din safe da yamma sannan ko yaushe a cikin zikirin Allah yake. Sannan ga yawan yin sadaqah, nafilfili da karatun Alkur’ani ga kuma iyayensa ko malumansa suna yi masa addu’a.

To irin wannan shine wanda ko shaidanun sun tafi nemansa bazasu taba ganinsa ba koda zasu duba fa’din duniya baki dayanta Allah bazai basu damar ganinsa ba.

Dama Allah ya fada a cikin Alkur’ani: “IDAN KANA KARANTA ALQUR’ANI MUNA SANYA KARIYA SHINGE MAI KAREWA ATSAKANINKA DA WADANNAN DA BASUYI IMANI DA RANAR LAHIRA BA”.

Na samu labarin ne akan shafin wani Balaraben Misra, (AL ISTISHFA) shine na fassara zuwa harahen hausa domin fadakar da al’umma su gane muhimmancin Azkar da karatun Alkur’ani mai girma.

Ya Allah ka kara kare mu da kariyar ka ka kuma tasare mu daga dukkan sharrin mai sharri albarkacin Manzon Allah SAW Amiin

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!