- Ga wasu kadan daga cikin amfanin sa wajen magance wasu cututtuka guda 10
- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer)
- Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai
- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.
- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa
- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa
- Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari
- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon shawara.
- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.
- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.
- Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.
Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!