Banned: Yadda Ake dawoda WhatsApp Dinda Aka Rufe Wato Akayi banned Dinshi
Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da warhaka, a yau zamuyi muku bayanine dan gane da WhatsApp din da akayi banned dinshi, hukumar WhatsApp wato kamfanin meta wanda suka hada WhatsApp da Facebook Instagram, suna yawan kulle account na mutane domin saba dokokinsu wanda wani lokacin mutum baima san wani doka ya karya ba kawai saidai yaga anyi banned dinshi.
Musamman masu amfani da GB WhatsApp koh FM dadai sauran ire-iren haramtattun WhatsApp messenger sannan za’a iya banned na normal WhatsApp ma da kake amfani dashi koh kuma WhatsApp business duk zasu iya indai ka saba dokokinsu koh mutane sukayi report dinka.
Wani lokacin akan kulle WhatsApp din na dan wani lokaci kaman misali ace 24hrs suce sai bayan awa ashirin da hudu sannan abude maka account dinka sannan akwai wanda kuma basa sa mai lokaci kawai zasuyi banning dinkane batareda ansa maka limit nacewa zaka dawo amfani da WhatsApp dinka ba.
Yadda zaka dawo da WhatsApp dinka idan an kulle kuwa shine dafarko akwai hanyoyi da yawa da zaka iya tuntuban WhatsApp game da matsalolinka koh banned da akayi maka za muyi amfani da contact form saboda idan an rufema WhatsApp zaka iya bin wannan hanyan.
Dafarko zaka shiga https://www.whatsapp.com/contact/?subject=messenger zai bude maka, idan ya bude maka saika cike wannan form din daki-daki inkazo wurin message saika cewa an banned 🚫🚫🚫 na WhatsApp dinka misali ”Hi there My WhatsApp number 08121252626 has been banned i think it’s a mistake” saika taba kan next step din daka gani a wajen.
Toh daganan kuma saika danna kan send question kana tabawa shikenan zai tafi zasu nunama thank you for sending message shikenan saika jira sako ta email dinka
Kana ganin haka toh ka jira sako ta email dinka da kasa lokacin cike form din shikenan ka gama WhatsApp dinka zai dawo in shaa Allah.