CIWON MARA LOKACIN AL’ADA (menstrual pain/cramps or dysmenorrhea )

Wasu matan in lokacin aladansu ya kusa to gaban su ya fara fadi kenan saboda sananin azaban ciwon da suke shiga kafin farawa da lokacin menses. Har gado ake badawa dalilin wannan ciwon mara saboda ciwon ya kan kama baya, mara, cinya, wani to lokacin harda amai, bacin ciki daa zawo. Musanman yara yan mata wanda suka fara a shekarun da bai kai 11yrs ba. Haka zalika yafi addaban mata yan kasa da shekaru 30yrs da wanda basu taba haihuwa ba. Ana kuma iya gada da kuma masu Shan ta Taba.. Dsss

A kowace zagayen wata ake yin al’adan, Ciwon mara na farawa ne kafin zuwan shi. A lokacin da kwai yake girma a ovary waton karamin mahaifa shi kuma babban mahaifa yana shirin tarfan wannan kwan in an samu ciki, shafin cikin shi na kumbura don kuwa tana nan neh Da aciki ke samun abinci da iska daga uwa. To in ba a samu ciki ba sai kwan da shafin cikin mahaifan duk su wanku su fito waje..

A wannan lokacin neh in mahaifar tana matsewa sai wasu hanyar jini su toshe, jini bai isa wasu sassan mahaifan. Rashin jini ya jawo rashin iska rashin iska ya janya tsanannin zafi.

Wannan ciwon normal ne amma akwai wasu condition da ke iya kawo sh…

Pelvic Inflammatory Disease… Wanda ake kiya da infection na mata. Duk da infection suna da yawa ana banbance su ne ta hanyar gwaji da alamomin su.

Endometriosis fitowan fatan cikin mahaifa a gunda bai da ce ba.

Fibroids

Adenomyosis shigar fatan mahaifa cikin nama (muscle)

Hanyoyin rage tsananin ciwon maran sun hada da.

Shan maganin zugi tare da bin shawarin likita.

Wanka da ruwan zafi ko duma maran da abu mai dumi.

Bed rest : Hutu.

kada asha abu mai caffeine ko gishiri sosai.

A rabu da shan taba ko giya.

Shan fruits.

motsa jiki akai akai ya na rage ciwon.

aje asbiti in ciwon bai raguwa.

Al’ada (menstruation) tana d fadi za mu dinga zakulu kadan kadan ana magana akai. Mata na bu katan ilimi sosai a wannnan fannin. Ya kamata mace ta san kwana nawa circle dinta yakeyi da abubuwan da yake affecting din shi dsss. Kuma ba nakasu bane al’ada kimar ya mace neh. Allah yasa mun amfana. Allah ya kara mana lafiya don lafiya arziki ce.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button