MAGANIN SANYI MAI RATSA JIKI DAKUMA ZAFIN SARKEWAR NUMFASHI
Mai fama da matsalar sanyi mai ratsa jiki,mura tari ko kuma zafin makoshi saiya nemi abubuwa kamar haka
- Ruwan lemun tsami
- Citta
- Zuma
- Tafasasshen ruwa
Atanadi ruwa tafasasshe sai a kankare cittar sannan sai a sanya cittar cikin ruwan sai a matsa rabin lemun tsami asanya zuma cikin karamin cokali sai bayan ya jiku kamar minti 10 zuwa 15 sannan arinka sha kamar ana shan shayi.
Za’a rinka yin irin wannan hadin anasha kullum har tsawon sati daya insha Allahu za’aga abin mamaki
Allah yasa mu dace
A turawa yan uwa su amfana.