DUNIYAR MA’AURATA

abu na farko da ya kamata ki sani kuma ki kiyaye shine daraja mijinki da kuma ganin girmansa da kimarsa, anan ina nufin kar ki kuskura ki fara kace nace da mijinki ta fannin zamantakewar auratayya kar wai dan kina ganin ya zama kamar abokinki ki rainashi, a’a anfi so mace ta zama tana bawa mijinta wani girma na daban acikin zuciyarta da kuma fili,

Na biyu kuma shine ki girmama iyayensa da yan uwansa tamkar yanda zaki girmama naki iyayen da yan uwan kar ki kuskura kiyi aiki da wannan karin maganar wacce hausawa ke cewa “‘ba a iya musu ya dangin miji”‘, duk namiji yana son a girmama iyayensa da yan uwansa,

Abu na uku shine ki zama mai mutukar hakuri da juriya agidan aurenki domin zaman aure zama ne na hakuri da kawaici, ki k’i ji ki k’i gani sai ki zauna lafiya da mijinki,

Abu na hudu kuma shine kar ki zama d’aya daga cikin matan nan masu bayyanar da sirrin mazajensu da sirrin gidan aurensu ga kawaye ko kuma abokan gaisawa hakan haramun ne,

Sai abu na biyar shine ki kasance mai tattalin dukiyar mijinki ma’ana banda almubazzaranci da kayan miji, ki kasance mai tattalin dukiyarsa da kayansa domin kowanne namiji yana k’in jinin yaga yasha wahala ya nemo abu sannan an wulakanta,

Abu na shida shine kar ki zama mai yawan bin k’wakk’wafin mijinki, komai yake yi idonki da kunnenki akai, kar ki zama haka domin maza basu kaunar mace mai bin diddigin abubuwan da suke yi,

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!