GA WANI SABON TALLAFIN KARATU GA MATASA DAGA GWAMNATI

Gwamnatin Buhari ta sanar da wani sabon tallafin karatu don amfanin matasa

Hukumar kula da rarar kudin man fetir, PTDF ta bayyana cewa daga sati mai zuwa za ta fara karbar takardar muradi daga daliban Najeriya masu bukatar hukumar ta tallafa musu akan karatunsu, inji rahoton jaridar Daily Trust. ta ruwaito hukumar na gayyatar daliban digiri na biyu da daliban digirin digirgir dasu fara aika mata takardunsu daga sati mai zuwa, ga masu sha’awar neman tallafin karatu a jami’o’in Najeriya.

Shugaban hukumar, Aliyu Gusau ne ya bayyana haka a yayin bikin rantsar da daliban digiri na biyu na digirigir da hukumar zata tura Birtaniya don karo karatu, inda yace wadanda za’a baiwa tallafin karatun a jami’o’in Najeriya zasu fi yawa fiye da na kasashen waje.

Gusau yace: “Daga sati mai zuwa zamu fara karbar bukatar daliban dake bukatar tallafin karo karatu, zamu sanar a shafukan jaridu, kuma zamu kai har watan Satumba muna sauraron mabukata.” Sai dai Gusau ya gargadi dalibai cewa hukumar ba zata lamunci tsawaita shekarun karatu ba daga bangaren dalibai, inda tace duk wanda ya wuce shekarunsa na karatu ba zai cigaba da samun tallafin ba.

Daliban da ake rantsar wadanda za’a tura su jami’o’in kasar Ingila sun hada da daliban digiri na biyu su 122, da masu digirindigirgir su 76, haka zalika yace hukumar ta rage jami’o’in hadin giwa na kasar Ingila daga 60 zuwa 15, don inganta tsarin tallafin karatu.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!