Har Yanzu Ana Cike Tallafin Bashi Na Smedan & Ja’iz Loan Cikin Sauki

A wani taro na manema labarai na bikin ranar MSME ta duniya na bana, da keda taken “Building a stronger future together” wanda ya gudana a ranar Litinin din da ta gabata a Abuja, Director general kuma shugaban kamfanin SMEDAN ya bayyana cewa kungiyar za ta fara raba Naira biliyan 1.2 a matsayin rance ga masu kananan sana’o’i, da matsakaitan masana’antu a fadin kasar nan tare da hadin gwiwar bankin JAiz.

Ya kara da cewa “A halin yanzu haka kungiyar SMEDAN na da kudade sama da Naira miliyan 600 a kasa sannan Bankin Jaiz ya tanadi Naira miliyan 600 wanda ke nufin akwai kusan Naira biliyan 1.2 daza a raba, kuma idan muka samu kason mu na bana daga Gwamnatin tarayya za mu fadada bada rancen”

Yanda Zaka Cike Rancen SMEDAN – Ja’iz Bank Loan.

1. Da farko zaka bude link na SMEDAN CIP 👉 https://cip.smedan.gov.ng

2. Sai ka zabi nau’in rancen da kakeso.
Akwai nau’ikan rance guda 4 a portal din.
* Personal Loans
* Mortgage Loans
* Business Loans
* Credit Loans

3. Sai ka zabi daya daga cikin irin rancen da kakeso, bayan ya budemaka zakaga (Loan purpose) wato manufar rancen, sai rukunin shekarunka (age group), sai matsayin aikinka (employee status), sai kuma idan kanason neman rancen a cikin jiharka ko duka jihohi sai ka zaba,  saika rubuta adadin rancenda kakeso sai ka danna “Check Availability”.

4. Anan za a nunamaka jerin bankunan da suke bada rancen da yadace da bayanan da ka saka a baya.

5. Sai ka zaɓi bankin da kakeso yabaka rancen amma zaifi ka zabi (Jaiz Bank) ta hanyar danna kan “View details and apply” domin da hadin kan bankin ne za a bada rancen.

6. Karanta duk bayanan da Abubuwan da ake bukata.

7. Sai ka cike bayanan da ake bukata wanda ya hada da: kasuwanci/sunan kamfani, sunanka, lambar wayar ka, jahar ka, adadin da kake bukata, smedan I.D, bayyana dalilin da ya sa kake bukatar rancen.

8. Sai ka danna “Submit”.

Idan ka cike rancen ka tabbatar kayi ajiye reference number.

Allàh bada sa’a.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!