HADIN DA YAKAMATA KIYI DA SANYINNAN DON KARIN NI’IMA A JIKINKI
HADI NA 1
Ki sami ganyen zogale ki wanke ki tabbatar babu datti saiki cocumber (gurji) ki fereshi ki yanyanka ki hada da ganyen Zogalen ki markade da blander saiki tace ruwan ,sai ki zuba madara da zuma aciki idan kinaso yayi sanyi ki saka a firij yayi sanyi lokacin shan ruwa kisha.
HADIN NI’IMA 2
- ‘ya’yan kankana
- Danyen gyada Mai kyau
- Dabino
- Alkama
- ‘ya’yan zogale
Sai ki hada ki dakesu gabadaya suyi laushi sosaii sai ki rinka Shan karamin cokali da Madara ta ruwa safe da yamma.