SABON HADIN SABAYA GA MATAN DA ZASUYI GYARAN YAYE KO SON YIN KIBA

Sabuwar Hanyar hadin Sabaya ga Matan da zasu yi yaye ko Matan dake fama da Rama

Dole ne duk inda mace take to ta matso kusa ta jarraba wannan hadin Insha Allah za tayi mamakin yadda jiki zai gyaru musamman Nonon da aka shayar da yaro.

Wannan hadin da za mu bada yana da matukar amfani ga jikin mace, amma sai masu hakuri da bin ka’idar sha ne kadai za su rabauta.

Abubuwan da za a bukata:-

  1. Waken suya gwangwani 4.
  2. Alkama gwangwani 4.
  3. Dawa gwangwani 4.
  4. Shinkafar tuwo gwangwani 4.
  5. Ridi gwangwani 4.
  6. Agushi gwangwani 4.
  7. Aya gwangwani 4.
  8. Gero gwangwani 4.
  9. Gyada me bargo gwangwani 4.
  10. Hulba gwangwani 2.

Duk abun dana lissafo kar a tambaye ni a soya dan ban ambaci suya a ciki ba.

Za a hade kayan dake sama tas bayan an tabbatar da tsaftacewa sai a nika suyi laushi sosai

Za a samu ruwa 75cl a dora wuta sai a debi garin da aka nika a dama da ruwa 25cl a zuba a kan ruwan dake wuta bayan ya tafasa, sai a rufe a bashi a kalla minti 10 zuwa 15 a tabbatar ya dahu a sauke a saka madara asha da safe kan aci komai da rana kan aci komai da dare in za a kwanta.

Ba a dafawa da yawa a ajiye zai tsinke. Idan miji na fama da rama ko rashin ruwan mani yana sha sau daya kullum idan yaro na rama ko za a yaye shi a bashi sau uku kullum idan be karbe shi ba yana saka shi kashi a cire hulba da madara Insha Allah zai dena.

Mata masu son kiba su sha matan da iya nono suke so ya gyaru su cire number 1 to 5 suyi ragowar.

Allah yasa a dace.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button