Hukumar kashe gobara ta kasa, Fire Service za su dibi sabbin ma’aikata na wannan shekara ta 2023
Hukumar CDCFIB wacce ta hada da Civil Defence, Immigration, Correctional da Fire Service, wanda suka bude portal din civil defence shekarar data gabata sannan suka bude portal din Immigration kwanaki, to yanzu ma zasu bude yanar gizon daukar ma’aikatan hukumar kashe gobara .
Kimanin Jami’ai 5,000 ne hukumar zata dauka, Saboda haka ga duk mai sha’awar wannan aiki kuma ya cika ka’idojin da ake bukata na neman wannan aiki to su hanzarta cikawa da zarar an bude Portal din ,da zarar an bude zamu sanar da alumma kamar yadda aka saba ace gaba da bibiyar mu ta wannan kafa.
Bayan zabe ita ma hukumar kula da gidajen yari ta kasa Nigerian Correctional Service (NCS🏚️) zata bude yanar gizon daukar ma’aikatan ita ma dubu biyar zasu dauka ,don haka masu bukatar sai su zama cikin shiri da zarar an bude zamu sanar da alumma a nema ko zaa dace .
Apply Now
©️Ahmed El-rufai Idris
Kaduna State Coordinator Zumunta Youth Awarenesses Forum