TA YAYA MIJINKI ZAI SO KI KAMAR YA HAUKACE?

Wata hira da ta gabata tsakanin wata tsohuwa yar shekara 50 da yar wata Jarida ta fito da sirrikan hakan:

Yar’jarida: Menene sirrun jin dadin zamantakewa tsakaninki da mijinki, Shin kin Kware ne wajen yi masa girki? Ko kuma Kyakyawace ke? ko dai kece uwar Iyalinsa?

Tsohuwa: Jin dadin zamantakewa tsakanin Ma’aurata dace ne daga Allah, amm mace na bada gudumawa wajen tabbatuwar haka, domin mace na iya maida gidan mijinta cikin walwala kamar yanda zata iya maidashi cikin kuncin rayuwa._
ba wai sai da kudi ba domin da yawa daga cikin mata masu kudi suna cikin kuncin rayuwa.

yawan ‘ya’ya ba shi ke kawo jin dadin rayuwa ba domin kuwa akwai macen da take da fiye da mazajen ‘ya’ya goma amma kullum cikin damuwa take kai ta iya yiwuwama mijin ya saketa a karshe.

daddadan Abinci kuwa bashi gida da maigida ke bukata ba da farko, sabo zaka ga mace tun safe har dare ba abin da take sai girki ga iya girkin amma kullum kukanta mijin baya kyautata mata.

Yar’jarida: To Menene Sirrin?

tsohuwa: Yayin da ran mijina ya baci shiru nake ina saurarenshi sauraro da ke cike da nutsuwa da nuna nadama akan abin da yake tuhumata dashi ina gyada kaina don nuna cewa ina sauraron bayanansa kuma na yarda dasu. Idan kika yi shirun kada ki kuskura ki rinka nuna masa cewa kece da gaskiya ko ya zalunceki a tuhumar da yake miki sabo da maza suna da mutukar tsikayen yanayi.

Yar’jarida: Me yasa bazaki fice ba idan ya fara fadan ki kyaleshi.

tsohuwa: Kar ki kuskura ki yi haka, sai ya ga kamar gudunshi kike ko maganganunshi basu dameki ba. Kawai ki yi shiru kina sauraran jawabansa kuma ki nuna yarda a duk abin da ya gaya miki har sai ya sauka daga fushinsa, sannan sai ki fita ki bashi wuri domin a lokacin jikinsa na bukatar ya dan huta kadan.

Yar’jarida: Daga nan kuma sai yaya? Zaki daina yi masa maganane tsawon kwanaki ko yaya?

tsohuwa: Kada ki gwada wannan halin domin kuwa sai ya saba da hakan a karshema ya fara cusguna miki ta hanyoyi.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!