Idan Wayarka Ta Fada Ruwa Ko Ta Jike Ga Yadda Zakayi Ka gyara:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, ayau zamuyi muku bayanine akan yadda zaka gyara wayarka idan ta fada a Ruwa, misali ka dauki ruwa zakayi amfani dashi sai wayar ta fada a cikin ruwan, sai kayi maza-maza ka cirota, toh a dai-dai lokacin daka cirota ta riga ta jike sharkaf da ruwan, toh mataki na farko da zaka dauka shine kacire batir din ta sanan ka tabbatar ba ka kunnata ba domin idan ka kunnata a wannan lokacin lallai za kayi damejinta. Ita kuwa matsala ta fadawar waya cikin ruwa wannan ku san ruwan dara ne wanda ke game da duniya baki daya, kusan wannan matsalan ta na damun mutane da dama, sannan kuma kowa da irin matakin da yake dauka, kusan rabin mutane da wannan matsalan take shafansu kokari suke yi subi hanyan da zasubi su iya tsane ita wayar tasu daga ruwan dake jikinta.

Wasu kuma wayar tasu nan take, take mutuwa saboda wasu ganganci da sukeyi bayan sun fito da wayar ta su a cikin ruwa, saboda haka duk wanda wayar shi ta fada cikin ruwa ya yi hanzari ya tsamo ta nan take ya cire murfin wayar ya kuma zare batir din ta, zai iya saka batir din a fili ko kuma wayar da batir din a fili yanda rana za ta gasa su, sanan kuma yana dakyau a lokacin da ka bude wayar ka cire batir kasake dubawa ka gani shin ruwan ya riga ya shiga har cikin injin wayar ko kuwa bai shiga ba? Toh idan har ka lura cewar ai ruwan ya shiga ciki zaka iya daukanta ka rike gefenta ka rika yarfeta kamar yadda ka ke yarfar da kaya idan an wanke su, za ka cigaba da yin haka har sai ka tabbatar cewar wayar babu sauran ruwa a cikin ta sannan ka sake mayar da ita cikin rana, ka kuma kifa bayanta a kasa, wato fuskanta yana kallon kasa bayanta na kallon sama saboda kada rana ya bata screen din wayar.

Toh idan kuwa ka fuskanci cewa lallai wayar ta jike sharkaf to abu na biyu shine ka sakata a cikin danyar shinkafa? Shinkafa? Na san da yawa zasuji abun banbarakwai me ya kawo kuma shinkafa a maganar tsane waya? Toh wannan haka yake, lallai shinkafa zata iya tsane maka dukkanin ruwan da wayar ka ta debo a cikinta, yadda zaka yi shine, zaka samu wani kwano mai girma wanda zai iya daukar wayar ka saka ta da batirin ta a gefe sai ka cika wannan kwanon da danyar shinkafar, ka sami murfi ka rufeta ruf, sai ka barta har tsawon awowi shida, daga nan sai ka daukota ka mayar da batirinta, idan ka kunna ta zata tashi da yardar Allah. (Wannan an jarabta kuma yayi aiki) Haka kuma mutum zai iya amfani da abin hura gashi wanda mata ke amfani da shi idan suka jika gashin kansu (Dryer) domin ya bushe, amma shima idan za’ayi amfani dashi dole a lura da wani irin dryer za’ayi amfani da shi, domin a lokacin da ka fuskanci cewar lallai wayar ka ta jike sosai har kana ganin cewa idan kayi anfani da danyar shinkafa ba zai iyi tsane ruwan ciki ba, toh ka ga a nan kana bukatar amfani da dryer, dafarko dai zaka cire batirin wayar sannan ka rike wayar a hannunka sosai sannan ka fara yarfadda ita kamar yadda ake yarfar da kaya da suka jike, bayan ka gama yarfarwa ka tabbatar da babu sauran ruwa a jikinta sai ka ciro ko kuma kaje shagon da ake yiwa mata gyaran gashi wato (saloon) kace su baka karamin dryer sannan kuma kayi amfani da mai sanyi ba mai zafi ba, domin idan ka yi amfani da mai zafi to zaka karawa wayar ka wata matsala ta daban, haka zaka ci gaba da busa mata iskar har sai ka tabbatar da wayar ta bushe sosai, sannan ka mayar da batirin sannan ka sakata a caji bayan wani tsawon lokaci sai ka kunnata, shiyasa yana da matukar kyau idan ka na da waya kuma ta na da tsada ko kuma halin gyara to yana da kyau ka rika saka mata irin rigunan ruwa da kuma abubuwan da zasu hanata lalacewa.

Wannan shine a takaice hanyoyin da zamu iya bi domin muga mun dawo da hayyacin wayarmu a lokacin da ta fada a cikin ruwa.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!